Tutorials

Yadda za’a sami kyautar MB Dari Biyar (500 MB) A Layin MTN

Advertisement Join Our Whatsapp Group

Assalamu Alaikum Yan uwa barkanmu da sake saduwa daku a cikin shirin namu na musamman wanda yake zuwa muku kai tsaye daga mujjalar Duniyan Fasaha, insha Allahu yau mun taho muku da wata sabuwar hanya da zaku bi wajen samun kyautar MB har 500 a layin MTN. wannan garabasar yana aiki a kowani wani irin layi na MTN. domin samun wannan garabasar akwai yan wasu hanyoyi da ya zamana dole a bi.

Abubuwan da ake bukata

•Wayar salula na Android (Android Smartphone) ko wace iri
•Mega Byte (Data or Mb)
•Mahajar MTN (mtn application) 👇👇

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.mtn1app&hl=en

Abu na fari da mutum ke bukata a nan shine wayar salula na Android, ya zamana dole mutum yana dauke da ita sabida akwai bukatar saukar da mahajar MTN wanda aka fi sani da MTN Application a turance wanda yana aikine kawai a wayar salula na Android. Za’a iya saukar da Mahajar MTN daga “play store” mai sune ‘My MTN’.

in shafin ya budu sai a danna mabullin “Dowload” sai saukar izuwa ga waya Bayan mutum ya saukar da wannan mahajar yana da bukatar budewa,

bayan an bude za’a ga jerin sunayen kasashe wanda kamfanin MTN ke aiki a wajen akwai bukatar mutum ya zabi kasar sa na Nigeria wanda yana can kusa da karshe a jerin sunayen.

Bayan mutum ya zabi kasar sa abu na gaba da zayyi anan shine sanya number wayar salulansa sai a latsa madannin “Proceed”

kamfanin MTN zasu turo maka da wani sako mai dauke da numbobi guda shida wanda ake kira da ‘OTP’ dole sai an sanya su a cikin akwatin da aka tanadar mai suna “Enter OPT” don tabbar da cewa wannan layin naka ne

muddin ansa wadannan numbobin daidai zai kaika izuwa ga sabo shafi. wasu lokutan ba dole sai ka sanya numbobin ba mudin sim na MTN din yana cikin wayar dazarar sakon ya iso zasu shigar da kansu sannan zai kaika izuwa ga wannan sabon shafin inda zai nuna sunan da akayi amfani dashi wajen register wannan layin da akasa.

Daidai kasan sunnan ka/ki ga wani karamin rubuta wanda ke dauke da “Yello you have been rewarded with 500mb free data Click here to activate” a turance ma’ana an baka kyautar Mb 500 ka lasta nan domin tabbatarwa

sai kayi yanda aka ce ta hanya latsa wannan sakon shikennan!!

Za’a iya amfani da wannan MB har tsahon awa ashirin da hudu (24 hours) za’a kuma iya shiga ko wani irin shafi kama daga Duniyan Fasaha, Google, Facebook, WhatsApp, YouTube da sauransu sannan kuma muddin an baka kada kasa ran samun wani ko sake bin matakan don dadawa sabida ana dabawa ne sau guda wa mutum.

Abun ban sha’awar anan shine Za’a iyawa mutane sama da dubu goma da waya daya in kuma kana da wani layi shima zaka iya masa koda yana cikin karamin wayane basai ka canza layin ba. sai dai akwai wani dan mataki da za’abi dan cin ma wannan manufa. Domin yi ma wasu ko wani layi sai a latsa wannan madannin sai a latsa “Switch User” zai mai da mutum izuwa ga shafin farko sai a bi matakan da suka gabata. Haka za’a ta maimai tawa. Allah ya bada sa’a.

Advertisement

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Advertisement
Back to top button
error: Alert: Content selection is disabled!!