Tutorials

Yadda zaku haɗe layinku na MTN da da Lambar NIN cikin sauƙi

Advertisement Join Our Whatsapp Group

Assalamu alaikum warahmatullah duba da halin da ake ciki na hukuncin da hukumar sadarwa ta ƙasa ta ɗauka na kulle layukan waya sama da miliyan 70 sakamakon rashin yin rajista da lambar zama cikakke ɗan ƙasa. Hakan ya jawo wasu da dama za su rasa layukan su saboda rashin mallakar lambar shaidar zama ɗan ƙasa.

Wasu kuwa suna da lambar zama ɗan ƙasa amma kuma basu san yadda zasu haɗe lambar da layin su ba. Shiyasa muka kawo muku wasu hanyoyi da kamfanin sadarwa na MTN ya fitar domin mutum ya haɗe layinsa da kuma lambar zama ɗan ƙasa.

Akwai hanyoyi da dama da kamfanin MTN ya samar domin masu amfani da shi su haɗe layinsu da lambar ɗan ƙasa ta NIN.

Yanzu babu sauran jira, babu zuwa bin layi kai da kanka kana zaune a gida, kasuwa ko wajen aiki zaka iya yi ta kan wayarka. Ga hanyoyin kamar haka;

  1. Kira: *785#
  2. SMS: ka aiki lambar NIN ɗinka zuwa ga 785
  3. Ka sauke manhajar MTN a wayarka.
  4. Ko ka ziyarci shafin mtn.ng/NIN

Ƴan uwa ku tayani isar da wannan saƙo ga sauran ƴan uwa domin suma su haɗe na su layin

Advertisement

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Advertisement
Back to top button
error: Alert: Content selection is disabled!!