Tutorials

Yadda Zaka Hada Layinka Da NIN Number Koda An Rufeshi

Advertisement Join Our Whatsapp Group

Jama’a Barkanmu da wannan lokaci Sannun mu da sake kasancewa daku a wannan shafin namu na HikimaTv.

Kamar de yadda kuka sani Gomnatin Nigeria ta umarci dukkan masu amfani da Layukan waya da suyi kokarin hada Layin nasu da katin dan kasa wato Nin number, wanda hukumar sadarwa ta Nigeria karkashin isa Ali pantami suka fitar da wannan tsarin hada number da nin domin samar da tsaro a nigeria.

Tun a wancan lokacin de mutane da dama sukayi ta kokarin hada layinsu da nin number, yayin da mutane miliyan 125 ne suka gabatar da rijistarsu ta NIN nasu don yin cudanya da su, yayin da mutane miliyan 78 suka samu damar yin Nin din.

Duk da tsawon lokacin da aka bayar domij kowane mai amfani da sim ya samu damar hada nasa da nin number, amma duk da hakan wasu basu hadaba.

Hakanne yasa Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da aiwatar da manufar daga ranar 4 ga Afrilu, 2022. Saboda haka, gwamnatin tarayya ta umurci dukkan kamfanonin sadarwa da su tsaurara matakan aiwatar da manufofin a kan dukkan wayoyin salula na zamani da aka fita a Najeriya

Hakanne yasa Aka fara rufe layukan da basu hada shi da nin number ba, Yayin da aka Rufe sama da Layuka miliyan 72 daga Ranar Litinin 04/4/2022.

A Yanzu de haka duk layin da ba,a hadashi da Nin number ba, a yanzu ya dena Kira, tura sako, amma zai karbi kira zai karbi sako sannan zaiyi Browsing.

Mutane dayawa sunyi Alhinin faruwar wannan lamarin, kasancewar layukansu an kullesu daga kiran waya da tura sako.

Duk da hakan har yanzu kana da damar da zaka hade Layinka da nin number, Amma Saide dole sai Sunan da yake kan Register layinka Yazo dede da Sunan da yake kan Nin number naka. Idan ba hakaba koda ka hada to bazai haduba, domin mutane dayawa sunyi hakanne suna zaton sun hade amma abun bai iyuba.

Domin ganin Yadda zaka hada Sim dinka da Nin number saika Shiga blue Rubutun da yake kasa

Shiga Nan Domin Hada Sim da NIN number

Allah ya bada Sa’a

Advertisement

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Advertisement
Back to top button
error: Alert: Content selection is disabled!!