Yanda ake yin formating a Computer
Assalamu Alaikum barkanmu da war haka bar kanmu da sake saduwa acikin sabon shirinmu daga hikimatv.ginsau.com wanda yau da izinin Allah zamu nuna muku yanda akeyin formatting na memory card daya samu matsala ta amfani da kwanfuta, sau da dama mu kan samu matsaloli a memory card namu ko kuma flash ko hard drive saboda masu dalilai na virus ko kuma baciwa sanadiyar sa a wani kwanfuta ko kuma waya. akwai kirkirarrun Applications da dama wadanda ake iya yin formating na kayan kwamfuta kamar Hard Disk, Memory, Pen Drive, Re-Writable CD ko DVD da dai makantansu, sannan da matakai mabanbanta da mutum zai bi domin ganin ya yi wannan formatting din cikin sauki amma kafin nan
MENE NE MA’ANARA FORMATING?
Formating shine goge dukkan abin da ke cikin abubuwan da ake iya yin ajiyar kayan kwamfuta. Misali Hard Disk, DISK, USB Flash, Memory da dai makamantansu, ta yadda za su kasance babu su a kwata-kwata a ciki.
MENE NE BANBANCI TSAKANIN SHI FORMATING DA KUMA DELETING?
Shi deleting ya na baka damar ka cire kaya wato file ko folder a cikin abu ne, shi kuwa formating yana kankare gabadayan kayan ka ne ta yadda koda akwai wani boyayyen abu kamar virus ko zai goge shi cikin sauki, sannan zai baka dama ka canza tsarin yadda shi drive din ya ke kallo files da suke shigowa cikinsa.
MATAKAN YIN FORMATTING MEMORY KO PEN DRIVE.
- Bayan ka saka USB Flash ɗinka a cikin ramin USB na kwanfutanka
sai ka shiga My Computer ko ta hanyar amfani da karamar hanya wato window + E
- Bayan ka shiga My Computer sai ka zaba shi USB Flash ɗin zaka iya gane shi ne ta ganin ƙarin babban mazubi da aka masa, ko kuma ta amfani da harafin da kwamfutan ka ba shi dashi ko kuma sunan shi Flash ɗin. Sai ka latsa shi da maɓallin dama wato(Right Click ).
- Zai fito maka da abubuwan zaɓi masu yawa sai ka taɓa Format. Zai buɗe maka ɗan ƙaramin Window da ake amfani da shi domin yin formating.
- Sai ka zaɓi NTFS a ramin File System.
- Ka zaɓi Quick Format domin yin kankarar cikin sauri.
- Sai ka taɓa maɓallin start zai tambayi amincewar kafin ya fara in ka tabbatar kana so kayi sai ka latsa mabullin ok ma’ana ka amince
- Zai fara yin formating ɗin ya danganci girman sa, amma baya jimawa. Abin kiyayewa shi ne, da zarar ka taɓa maɓallin formattting dole ka barshi ya kammala idan ba haka ba, ka cireshi ko kuma wata matsala ta faru na ɗaukewar kwamfutar ko mutuwa to zaka iya rasa USB Flash ko memory card naka ɗin gaba ɗaya. Dafatan mun sami wannan post din da muhimmanci, ku tayamu sharing ta whatsapp facebook twitter da kuma Instagram dan yan uwanku su amfana.