Tutorials

Hatsarin Dake Cikin Siyan Sabuwar Waya Ko Second Hand A Rayuwar Mu Ta Yau

Advertisement Join Our Whatsapp Group

Ba sabon abon abu bane damfara a wannan lokaci da muke ciki, sannan kuma damfara ta kasu kashi daban-daban, da zarar antoshe wannan kafar sai kuma ma-damfaran su sake nimo wani hanyar domin aikata mugun nufinsu.

A yau damfara ta hanyar siyan sabuwar waya ko kuma second hand a kasuwa ba ainihin shagon kamfanin wayar ba ya zama “Ruwan dare gama duniya”. Wanda hakan ya faru akan wasu da nasani.

Dalilin wannan rubutu shine, domin hankaltarwa da kuma nusar damu illar wannan matsala da mutane suke fuskanta batare da sanin su ba hakan kuma yake faruwa.

Da farko akwai:

EASYBUY.

°° EasyBuy shine: wani sabon hanyar mallakar WAYAR-HANNU ta hanyar bashi tare da kudin ruwa a ciki, ma’ana; dole ne kabiya kudi kashi talatin 30% na adadin kudin wayar, sannan kuma za kaje da shaidu Abokai ko Yan-Uwa guda hudu domin tabbatarwa, sai kuma zaka dinga biya ƙada-ƙadan har ka gama biya.
NB: sharadin su shine zasu saka maka wani “Security Plugin” a cikin wayar wanda shine zai zama tsani zakaninka da su (Easybuy din) wannan plugin din aikinsa shine: zayarwa ko dakatar da wayarka daga yin aiki ko kuma kulleta ma gaba daya ko turama mutanen dakake da lambobinsu saƙon cewa kaci bashi baka biya ba Dss.
Na Biyu:.

PALMPAY

°° Palmpay: shima kamar EasyBuy ne tahanyar sakawa waya “Security Plugin” amma sun sha bamban.
Palmpay shi ƙaramin banki ne da masu amfani dashi suke hada-hadar sakawa da cirewar kudi da kuma biyan katin wuta, ruwa, waya, Dss. Suma suna bada bashi wanda in suka baka zasu saka maka “SECURITY PLUGIN” irin na EASYBUY idan baka biya ba shima zasuyi maka kamar yanda na zayyana a sama.

Shin Tayaya Ake Damfara Ta Wannan Hanyar Kamar Yanda Na Ambata a Farkon Maƙalar?

~ Yanzu Madamfara suna aikata daya daga cikin EASYBUY ko Bashin PALMPAY, in sun siya wayar ko bashin kenan ansaka musu “SECURITY PLUGIN” a ciki, to dama ba sunci bashin bane ko siyan wayar domin su biya kawai domin cutar bayin Allah ne da basuji ba basu gani ba, ta hanyar siyar musu da wayar domin kar su biya bashin kai da kasiya kai ne abun zai shafa. Sai a kula.

Shin Tayaya Zangane Ko Wayata Tana Da Wannan Security Plugin Din?

Ta hanyar shiga SETTING na wayarka sai kuma ka shiga SECURITY & LOCATION sai kayi ƙasa can zakaga inda aka rubuta DEVICE ADMIN APPS to anan zakaga an rubuta SECURITY PLUGIN (duba ƙasan domin ganin hoton SECURITY PLUGIN domin kare kanka daga faɗawa hannun macuta)

Sai a kula domin tsira da kudi da kuma mutunci, domin wannan shine sabuwar hanyar cutarwarsu.

3-9-2022
Cc Basiru Ismail

Advertisement

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Advertisement
Back to top button
error: Alert: Content selection is disabled!!