Yadda Zaka Dawo Da Duk Wani Application Daka Dauko Daga Cikin Playstore Zuwa Kan Wayarka ( File Manager ).
Yadda Zaka Dawo Da Duk Wani Application Daka Dauko Daga Cikin Playstore Zuwa Kan Wayarka ( File Manager ).
Jama,a Assalamu Alaikum Barkanmu Da Wannan Lokaci Sannunmu Da Sake Saduwa Daku A Cikin Wannan Shafi Namu Mai Tarin Albarka Wato Hikimatv.
A Darasin Namu Nayau Batare Da Wani Bata Lokaci Ba, Zamu Kawo Muku Cikakken Bayani Akan Minene Playstore Sannan Wane Dalili Ne Yasa Playstore Basa Barin App Yahau Kan File Manager Ko Internal Storage Na Wayarka A Duk Lokacin Da Ka Saukar Dashi Daga Cikin Playstore Din.
Ku Karanta Wannan Bayani A Nutse Domin Fahimtar Yadda Abin Yake Dalla-dalla domin tsallake Wani Wurin Zai Barka Cikin duhu da Rashin Ganewa.
Da Farko Abinda Yakamata Kasani Kariga Kasani Wannan Abu Kuwa Ba Komai Bane Face Duk Wani Application Daka Saukar Dashi Daga Google Ko Aka Turama To Kana Iya Samunsa Akan Wayarka Koda Ka Gogeshi Ta Cikin Menu Din Kan Wayar Taka.
Dalilin Dayasa Nayi Wannan Bayani Shine Wani Lokacin Zakaga Mutum Yayi Uninstall Na Wani Application Amma Kuma Daga Baya Saiya Dawo Yana Bukatar Ya Kara Install Na Wannan Application Amma Kuma Babu Dama Saboda A Iya Cikin Wayarsa Yake Babu Shi Akan Memory Ko Phone Na Wayartasa.
To Akwai Hanyoyi Guda Biyu Da Akebi Wurin Tabbayar Dacewar Wannan Application Ya Zauna Akan Wayarka Na Har Abada Ko Har Lokacin Da Kaje Da Kanka Ka Gogeshi.
A Wayoyinmu Na Baya Duk Application Din Da Aka Tura Mana Muna Iya Ganinsu Daga Baya Koda Kuwa Munyi Installing Dinsu Daga Cikin Zendar Din Kan Wayartamu.
To Amma Yanzu Da Akasamu Update Da Dama Sai Yazamana Idan Kayi Installing Na Application Daga Cikin Zendar Dinka To Bazaka Samu Wannan Application Akan Memory Din Kan Wayarka Ko Na Internal Storage Ba.
To Haka Zalika Suma Application Din Daka Saukar Daga Google Playstore Basa Hawa Kan Memory Ko Internal Storage Iyakaci Ka Gansu A Cikin Main Menu Nakan Wayarka.
Kaga Kenan Da Zarar Ka Gogesu To Sun Bar Kan Wayarka Har Abada, Wanda Nasan Mutane Da Dama Kuma Suna Dawowa Su Bukaci Wannan Application Daga Baya.
Idan Harka Gogeshi To Ka Rasashi Kenan Har Abada Ta Yadda Sai Dai Ka Saukar Da Wani Daga Playstore Daga Baya.
To Domin Magance Wannan Matsala Zamu Ajiye Muku Link Na Wani Application Wanda Da Zarar Ka Saukar Da Wani Application Da Kake Tunanin Zaka Kara Yin Amfani Dashi Anan Gaba To Saikayi Amfani Da Wannan App.
A Cikin Wannan Application Zakaga Duk Wani Applications Dake Kan Wayarka, To Anan Zaka Iya Taba Wanda Kakeso Yadawo Kan Wayarka, Idan Kuma Biyu Ne Ko Uku Ko Goma Duk Zaka Iya Makin Dinsu Saika Danna Backup.
Kana Dannawa Wadannan Applications Zasu Koma Kan Wayarka Wato Internal Storage Ko Kuma Kan Memory Din Kan Wayarka Zasu Iya Tambayarka Inda Kakeso Wadannan Application Su Rika Komawa A Duk Lokacin Daka Bukaci Hakan.
To Idan Kuma Takan Zendar Ne Idan An Turama Wani Abu Ko Wani Application Wanda Kaga Zaka Iya Nemansa Daga Baya To Saika Fita Ka Koma Takan File Manager Ko Internal Storage Kayi Installing Dinsa To Zai Zauna Akan Wayarka Koda Kuwa Ka Gogeshi Ta Main Menu, To Idanka Dawo Kan Wayarka Zaka Sameshi Kuma Ka Kara Installing Dinsa.
Mungode Mungode Ga Link Din Application Din Nan Saika Danna Wurin Da Aka Rubuta Download Now Domin Sauke Wannan Manhaja Cikin Sauki.