Tutorials

Yadda Zaka Hana Kowane Kira Shigowa Cikin Wayarka Batare Da Ka Kashe Wayarka Ba.

Advertisement Join Our Whatsapp Group

Yadda Zaka Hana Kowane Kiran Waya Shigowa Cikin Wayarka Batare Da Ka Kashe Wayarka Ba.

Jama,a Assalamu Alaikum Barkanmu Da Wannan Lokaci Sannunmu Da Sake Saduwa Daku A Cikin Wannan Shafi Namu Mai Albarka Hikimatv.

A Darasin Namu Nayau Zamu Kawo Muku Cikakken Bayani Akan Yadda Zakayi Wannan Abu Amma Kafin Mukai Ga Kawo Muku Cikakken Wannan Bayani Muna Fatan Zaku.

Karanta Wannan Bayani A Nutse Kuma Tundaga Farko Har Karshe Domin Fahimtar Yadda Abin Yake Dalla Dalla.

Sanin Kanku Ne Mutane Da Dama A Wasu Lokutan Suna Shiga Wani Yanayi Wanda A Wannan Yanayi Ko Lokaci Basa Son Akirasu Ko.

To Wannan Yana Sa Wani Lokaci Sai Kaga Mutum Cikin Yanayi Na Damuwa Saboda Baya So Yakashe Wayarsa Sannan Kuma Baya So A Kirashi.

To Idan Hakan Ta Kasance Akwai Wata Hanya Da Muka Lalubo Muku Domin Kusamu Saukin Wannan Matsala.

Sannan Wannan Abu Zamu Koya Muku Shine Batare Da Kayi Amfani Da Wani Application Ba.

To Da Farko Dai Abinda Yakamata Kayi Shine Zaka Nemo Phone Na Cikin Wayarka, Daga Sama Saika Danna Wani Wuri Da Aka Yi Alamar … Guda Uku Daga Sama Hannun Dama.

Idan Ka Danna Wannan Wuri Zakaga Wurin Da Aka Rubuta Block Calls, To Saika Danna Wannan Wuri To Anan Saika Danna Wurin Blocked Calls To Anan Zaka Iya Zaban Sim 1 Ko 2 Kake Son Rufewa Ko Kuma Kowane Sim Zaka Rufe.

To Idan Ka Rufesu Duk Kiran Da Akayima A Waya Bazai Shigoba Kuma Gashi Wayarka A Bude Ba,a Rufeba.

Mungode Mungode Dukka-dukka Anan Muka Kawo Karshen Wannan Darasi Inda Muke Fatan Zaku Kasance Da Wannan Shafi Namu Mai Albarka Domin Samun Sababbin Shirye-shiryenmu Akowane Lokaci.

Advertisement

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Advertisement
Back to top button
error: Alert: Content selection is disabled!!