Tutorials

Yadda Zaka Dauko Film Din Da Baka San Sunansa Ba Ta Hanyar Amfani Da Wani Hoto Daga Cikin Wannan Film.

Advertisement Join Our Whatsapp Group

Jama,a Assalamu Alaikum Barkanmu Da Warhaka Sannunmu Da Sake Saduwa Daku A Cikin Wannan Shafi Namu Mai Albarka Hikimatv.

A Darasin Da Zamu Koyar Daku A Yau Zamu Kawo Muku Cikakken Bayani Akan Wata Sabuwar Hanya Dazakabi Idan Kanaso Kasan Sunan Wani Film Wanda A Baya Baka San Sunansaba.

Misali Zaka Iya Samun Guntun Film Ko Video Batare Da An Rubuta Sunan Wannan Film Ba, Kuma Saiya Kasance Kaji Kana Matukar Son Kasan Sunan Wannan Film Harma Ka Saukar Dashi Akan Wayarka.

Amma Kuma Saiya Kasance Baka San Sunan Wannan Film Ba, To A Yau Munyi Kokari Inda Muka Zakulo Muku Wata Sabuwar Hanya Wanda Zaka Samu Karin Bayani Akan Yadda Zakabi Wata Hanya Domin Gano Sunan Wannan Film.

Sai Dai Wannan Bayani Lalube Ne A Cikin Duhu Domin Za,a Iya Baka Sunan Wannan Actress Ko Acto, Abinda Dai Ake Bukata Shine, Yakasance Hoton Daka Dauka Na Actor Ne Ko Actress.

Idan Kayi Screenshot Na Hoton Saikayi Crop Dinsa, Wato Ka Yankeshi Yazama Dai Dai Da Dai Dai, Bayan Kayi Haka Kai Tsaye Saika Tafi Kan Manhjar Google Chrome.

Kana Hawa Kan Wannan Browser Din Saika Duba Daga Gefen Hannunka Na Dama Zakaga Wani Wuri Mai Alamar Camera, Idan Kuma Babu To Saikayi Update Na Chrome Din A Playstore.

Bayan Kataba Wannan Wuri Mai Alamar Camera, Zaikaka Zuwa Kan File Manager Din Kan Wayarka, Yana Kaika Saika Taba Kan Hoton Dakayi Screenshot.

Kana Tabawa Zakaga Wani Wuri Daga Kasa An Rubuta Search Saika Danna Wannan Wuri Take Zai Watsoma Dukkan Bayani Akan Wannan Hoton.

Abu Na Farko Zai Watsoma Sunan Wanda Kayi Searching Walau Mace Ko Namiji, Bayanan Zai Watsoma Fina Finan Da Wannan Actor Ko Actress Tayi.

To A Inda Matsalar Take Shine Baka San Sunan Wannan Film Ba, Ahalin Zasu Watsoma Sunayen Film Da Dama To Dabarar Da Zakayi Anan Guda Dayace.

Zaka Rika Daukan Sunayen Wadannan Fina Finai Kana Rubutawa A Youtube Suna Baka Film Din Kana Dubawa A Haka Har Ka Gano Wane Film Ne.

To Kaga Kai Tsaye Saika Rubuta Sunan Film Din Ka Saukar Dashi Akan Wayarka Batare Da Wani Tunani Ko Shiga Cikin Wata Matsalaba.

Mungode Mungode Mungode Inda Dukka Dukka Anan Muka Kawo Karshen Wannan Darasi Inda Muke Fatan Zaku Kasance Da Wannan Tasha Tamu Mai Albarka Hikimatv Domin Samun Sabbin Shirye-shiryenmu Akowane Lokaci.

Advertisement

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Advertisement
Check Also
Close
Back to top button
error: Alert: Content selection is disabled!!