Tutorials

Yadda Zaka Chanza Background Na Kowane Irin Hoto A Wayanka Ta Android Ta Hanyar Amfani Da Remove Bg.

Advertisement Join Our Whatsapp Group

Jama,a Assalamu Alaikum Barkanmu Da Wannan Lokaci Sannunmu Da Sake Saduwa Daku A Cikin Wannan Site Namu Mai Suna Hikimatv.

Dafatan Kuna Cikin Koshin Lafiya Kamar Yadda Muke Ciki Ameen Summa Ameen.

A Posting Dunmu Nayau Zamu Kawo Muku Cikakken Bayani Akan Yadda Zaka Sanja Background Na Hoto Kai Tsaye Batare Da Wani Bata Lokaci Ba.

Menene Background ? background Dai Shine Ainishin Wurin Da Kadau Hoto Misali Zaka Iya Daukan Hoto A Cikin Gidanku, Saiya Kasance Wannan Wuri Daka Dau Wannan Hoto Baiyi Kyau Sosai Ba.

To Kana Da Zabin Yadda Zaka Sanja Wannan Wuri Domin Su Kansu Yan Film Da Mawaka Dama Sauran Sanannun Mutane Suna Amfani Ne Da Wannan Application Na Background Changer Wurin Sanja Wurin Da Suka Dau Ko Aka Musu Hoto.

To A Cikin Bayanin Dazamu Kawo Muku Yau Zamu Ajiye Muku Link Din Wannan Application Mai Suna Remove Bg Domin Kusamu Hanya Mai Sauki Wurin Aiki Da Wannan Application.

Amma Kafin Mukai Ga Ajiye Muku Link Din Wannan Application Yakamata Kasan Da Wannan Matsalar Ko Kasan Wannan Bayanin.

Shi Aikin Cire Background Na Hoton Yarabu Gida Biyu Ana Iya Yinsa Ta Website Wato Kaje Google Ka Rubuta ” Removebg” Ko Kuma Ka Saukar Da Application Dinsa Akan Wayarka Ta Hanyar Danna Kan Link Din Dazamu Ajiye Muku.

To Yanzu Kasancewar Munyi Alkawarin Ajiye Muku Link Ne Bari Mu Muku Bayani Da Application Din Ko Muce Yadda Zakayi Remove Na Background Din Ta Hanyar Amfani Da Application Din Bata Website Dinba.

To Da Farko Dai Bayan Ka Danna Kan Link Din Da Muka Ajiye Muku Kayi Download Na Wannan Application Sai Kayi Installing Dinsa, Bayan Kayi Installing Sai Kayi Open To Daga Nan Kuma Saika Danna Wurin Da Aka Rubuta.

“Upload Image” Daga Nan Zai Kawoka Shafi Na Gaba Inda Anan Kuma Zaka Gallery Ko Image, To Anan Anaso Ne Kazabi Wanda Zaka Bude Hotunan Da Suke Kan Wayarka.

To Bayan Ka Zaba, Za, a Watsoma Hotunan Da Suke Cikin Wayarka Gaba Daya To Kai Kariga Kasan Inda Ka Ajiye Hotunan Da Kake Son Sanja Musu Wannan Background Din To Anan Saika Danna Kan Hoton Daga Nan Zai Kawoka Izuwa Shafi Na Gaba.

Inda Anan Kuma Zakaga Option Guda Hudu ( 4 ) Wato Zabi Guda Hudu.

Zabi Na Farko Dai Shine Zakaga Hoton Daka Zaba Ansanja Mar Kala Yakoma Kamar Potrait Wato Yayi Dishi Dishi, Anan Zaka Iya Zaban Wanda Kake So.

Zabi Na Biyu Kuma Zakaga An Dorama Hoton Akan Wasu Background Masu Yau To A Cikin Wadannan Idan Akwai Wanda Yama Zaka Iya Zaba.

Ana Uku Kuma Zakaga Hotunan Naka Akan Kaloli Kamar , Bakin Background, Jan Background, Da Kuma Fari Da Dai Sauransu To Anan Ma Idan Akwai Wanda Kakeso Zaka Iya Zaba Kataba Wurin Da Aka Rubuta Download Idan Kuma Babu Wanda Yama To Daga Hannun Hagu Zakaga Wurin Da Aka Rubuta “Upload Background” Wato Suna Nufin Idan Kana Da Wani Wuri Mai Kyau A Cikin Wayarka To Kadauko Wannan Wuri Domin Ka Dora Hotonka Akai.

Sai Dai Bayan Ka Dauko Hoton Daga Kan Wayarka Zai Kawoka Wani Wuri Inda Zakaga Yadauke Wancan Backgraound Din Na Farko To Daga Hannun Dama A Kan Hoton Zaka Inda Aka Rubuta ” Edit ” To Saika Danna Wannan Wuri Daga Nan Kuma Zai Kaika Shafi Na Gaba Inda Zaka Zabi Background Din Da Kake Bukata.

Ga Link Din Application Din Saiku Saukar Dashi Zuwa Kan Wayoyinku Domin Samun Sauki Wurin Sanja Duk Wani Background Da Kuke Bukata A Cikin Wayoyinku Na Android.

Advertisement

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Advertisement
Back to top button
error: Alert: Content selection is disabled!!