Yadda Zaka Dunga Ganin duk Inda Budurwarka take Shiga A Wayar Ta
Assalamu Alaikum Warahamatullah Barkanmu da sake kasancewa daku a wannan shafin namu mai Albarka Na HikimaTv.
A yau nazo muku da wani bayani akan yadda zaku dinga ganin duk inda budurwar ka ko matarka ko yayanka suke shiga da wayar su koda kuwa sun goge Record ko history na inda suka shigan.
Wani lokacin kana iya hana budurwarka ko kanwarka ko yayanka yin wani abun a waya kamar chat ko browser kode wani abu marar kyau, amma duk da hakan sai suje suyi a boye ba tare daka saniba, wanda yin hakan da sukeyi abune marar kyau.
Dan haka idan irin hakan tana faruwa, to ga yadda zakayi domin ka gano ina suke shiga acikin wayar su.
Da farko zaka karbi wayar wanda kakeso kaga inda yake shigan.
Saika shiga browser ta wayarsa kamar google chrome.
Idan ka bude browser saika shiga wajen da akeyin Rubutu a browser wato wajen search, saika Rubuta Google Activity
Daga nan saika danna alamar nema wati search, nan take zakaga ya bude ya kawo maka wasu rubutu, saika duba Inda aka Rubuta Welcome to My Activity
Saika shiga wajen daga nan zai kawo maka wani shafi wanda anan ne zakaga duk inda mutun ya shiga acikin wayarsa, da kuma lolacin daya shiga.
Shikkenan saika duba ka gani domin kadau mataki akan abun daka gani idan marar kyau ne.
Allah ya taimaka.