Loan & Support

Ga wata Sabuwar Dama Ga Matasan Nigeria Daga Ministry of External Affairs

Advertisement Join Our Whatsapp Group

Assalamu alaikuma warahamatullah, barkanmu da sake kasancewa daku a wannan shafin namu mai Albarka na hikimav.

A yau na sake zuwa muku da wata sabuwar dama ga dukkan matasan nigeria maza da kuma mata.

Gwamnatin India ta ƙarƙashin Ministry of External Affairs zata bawa ƴan Africa damar yin karatun online degree na farko da kuma na biyu (Masters degree) kyauta (100% scholarship) daga manyan jami’o’i daban-daban na ƙasar

kamar irinsu:

  • Lovely Professional University (LPU), Indira Gandhi National Open University, Chandigarh University,
  • Guru Jhambheswar University of Science and Technology,
  • Aligarh Muslim University,
  • da sauransu.

Zasu baka damar yin karatun a fannoni daban-daban kamar:

  • Science, Commerce,
  • Computer Science,
  • Management,
  • Economics,
  • Languages,
  • Humanities and Arts,
  • da sauransu.

Da farko sun sanya international passport ya zama dole saida shi mutum zai iya cikewa, amma sakamakon ƙorafe-ƙorafe da akayi musu sun maidashi optional, ba dole bane yanzu. Katin zama ɗan ƙasa (National identity card) ya wadatar.

Wannan dama ce babba da ya kamata ƴan uwa na ƴan Arewa suyi amfani da ita tun kafin ta kuɓuce mana.

Degreen su iri ɗaya ne da na National Open University (NOUN), zan iya ce maka ma yafi nasu daraja domin shi wannan is recognized worldwide.

Indai kana da lokacin da zaka hau Facebook, Whatsapp, twitter, dss, to ina tabbatar maka kasuwancin ka bazai hanaka yin wannan karatun ba.

Da farko sun sanya 31st July, 2022 ta zama itace ranar ƙarshe, amman saboda maslaha sunyi extending ɗin died-line ɗin har zuwa 15th August, 2022. (yau saura sati biyu su rufe).

Wani abun burgewa da wannan degreen shine, a cikin shekara uku zaka gama, kuma babu ruwanka da yajin aiki (strike).

Danna Link din kasa don Cikawa

Shigo nan don Cikawa

Allah taimaka

Advertisement

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Advertisement
Back to top button
error: Alert: Content selection is disabled!!