Ga Wata Sabuwar Dama Daga Tashar Arewa24
Assalamu Alaikum barkanmu da wannan lokaci da fatan kowa yana cikin koshin lpy
A yau nazo muku da wata sabuwar dama daga gidan bidiyo na tashar Arewa24
Kamar yadda kuka sani tashar AREWA24 itace gidan talabijin din nishadantarwa ta farko mai yada shirye-shiryenta 24 da harshen Hausa wacce aka kirkira don masu jin yaren Hausa.
Wannan tashar tana jihar Kano, Nigeria, a halin yanzu AREWA24 tana da shirye-shirye guda 11 na kashin kanta da suka kunshi nishadantarwa da rayuwar yau da kullum duk a harshen Hausa.
Sannan Burin AREWA24 shine ta fito da kyawawan manufofi, tsari, banbance-banbance, girma da kuma nagartar masu jin yaren Hausa a dukkan fadin Nigeria da kasashen da suke makwabtaka da ita kuma ta hada kan masu jin yaren Hausa waje daya a ko ina suke a karkashin inuwar AREWA24
A yanzu haka wannan gidan talabijin na arewa24 zasu dauki ma’aikata na tsare-tsare na wasanni da bincike na musamman don kara wayar da kan jama’a, inganta kokarin Tallace-tallace, nazarin ma’auni na kafofin watsa labarun da haɓaka tallace-tallace na AREWA24 da sauran ayyukan kasuwanci na AREWA24.
Wannan damace da matasa masu bukatar yin aiki a Arewa24:
Domin Neman wannan aikin saika Shiga Link din da yake kasa:
Shigo nan domin Cikawa
Allah ya bada sa’a Ameen