Yadda Zaka Gano Duk Wata Matsalar Dake Damun Wayarka Ta Hanyar Amfani Da Phone Doctor.
Yadda Zaka Gano Duk Wata Matsalar Dake Damun Wayarka Ta Hanyar Amfani Da Phone Doctor.
Jama,a Assalamu Alaikum Barkanmu Da Wannan Lokaci Sannunmu Da Sake Jamewa Daku A Cikin Wannan Shafi Namu Mai Tarin Albarka Hikimatv.
Inda A Cikin Darasin Namu Nayau Zamu Kawo Muku Cikakken Bayani Akan Wata Manhaja Mai Matukar Amfani Wanda Zakuyi Farin Ciki Da Samunta.
Ita Dai Wannan Manhaja Zata Taimaka Muku Ne Ta Wajen Baku Cikakken Bayanai Akan Matsalolin Dake Damun Wayarku Batare Da Kunsani Ba.
Wani Lokacin Zakaga Wata Matsala Tana Damun Wayar Mutum Irin Daukan Zafi Yawan Cin Chaji, Ko Shan Data Amma Baima San Wannan Matsala Na Damun Wayarsaba, Saboda Yana Da Kudin Da Yake Sayen Datar Yadda Yagadama.
Wani Lokacin Kuma Wayarka Tana Iya Debo Cutar Bayiros Batare Da Cewar Kasani Ba Kuma Hakan Na Faruwa Ne Saboda Rashin Sani Ko Rashin Samun Abinda Zaina Tunatar Dakai.
To Wannan Dalili Yasa A Yau Mukayi Kokari Muka Zakulo Muku Wannan Application Wanda Idanma Baka San Abinda Ke Damun Wayarkaba To Wannan Application Zaiyi Scanning Din Wayartaka Tare Da Bayyana Maka Dukkan Abubuwan Da Wata Matsala Ke Damunsu.
Saboda Haka Ne Muke Fatan Zakuci Gaba Da Karanta Wannan Bayani Tun Daga Farko Har Karshe Domin Fahimtar Yadda Abin Yake.
Domin Kuskure Daya Zakayi Abin Yaki Baka Yadda Kake So, Sannan Muna Rokon Daku Rika Danna Alamar Allow Na Notifictaion Domin Samun Sabbin Darussan Da Muke Dorawa Akowane Lokaci.
To Da Farko Dai Zamu Ajiye Muku Link Din Wannan Manhaja A Kasa Domin Kusamu Damar Saukar Da Ita Akan Wayoyinku Cikin Sauki Batare Da Kunje Wani Waje Nemanta Ba.
Bayan Kun Saukar Da Wannan Manhaja Izuwa Kan Wayoyinku, Saikuyi Intall Nata, Sannan Kuyi Open.
Daga Nan Zata Tambayi A Bata Dama Saika Danna Wani Dan Box Daga Kasa Saika Danna Allow Ko Submit Kai Koma Dai Mi Sukace Ka Danna Saika Danna.
Daga Nan Kai Tsaye Wannan Manhaja Zata Daukewa Izuwa Cikinta Inda A Home Dinta Daga Sama Zakaga Wani Wuri Da Akayi Alamar Play.
Daga Kasa Kuma Anyi List Na Duk Wani Apps Dake Cikin Wayarka Da Wanda Kasani Dama Wanda Baka Sani Ba.
To Anan Saika Danna Wannan Wuri Mai Alamar Play To Nan Take Zai Fara Searching Na Duk Wani Apps Dake Kan Wayarka.
Idan Yagama Zai Fitarma Da Duk Wasu Matsaloli Dake Damun Wayarka, Idan Zafi Take Dauka Zai Nunama, Idan Bayiros Ne Akai Zai Nunama Haka Zalika Idan Wayarka Chaji Take Yawan Sha To Zai Nunama.
Kuma A Lokacin Da Kafara Wannan Scan Din Idan Abu Da Matsala A Kansa To Zaiyi Jar Yana Nunama Cewar Wannan Abun Akwai Matsala A Tare Dashi.
To Daga Baya Zaka Iya Sanin Abinda Yakamata Kayi Amma Kasani Akwai System Applications Wadanda Ba,a Gogesu Idan Har Sune Suke Baka Matsala To Saidai Ka Saida Wayar A Takaice Saboda Ka Rika Haduwa Da Wannan Matsala.
Mungode Mungode Sai Mun Hadu Daku A Cikin Wani Sabon Darasi Anan Gaba Inda Muke Fatan Zaku Kasance Da Wannan Shafi Namu Mai Albarka Domin Samun Sabbin Shirye-shiryenmu Akowane Lokaci.
Ga Link Din Wannan App Ko Muce Manhaja Saiku Danna Wurin Da Aka Rubuta Download Now Domin Saukar Dashi Akan Wayoyinku Cikin Sauki.