Tutorials

Ire Iren Whatsapp Din Da Amfani Dasu Yake Da Hadari Ga Account Din Mutum Dama Number Din Wayarsa.

Advertisement Join Our Whatsapp Group

Ire Iren Whatsapp Din Da Amfani Dasu Yake Da Hadari Ga Account Din Mutum Dama Numer Din Wayarsa.

Jama,a Assalamu Alaikum Barkanmu Da Wannan Lokaci Sannunmu Da Sake Saduwa Daku A Cikin Wannan Shafi Namu Mai Albarka Hikimatv.

Inda Muke Fatan Zaku Danna Alamar Allow Na Notification Din Dake Cikin Wannan Shafi Namu Domin Samun Sababbin Shirye-shiryenmu Akowa Wane Lokaci.

To A Cikin Darasin Namu Nayau Zamu Kawo Muku Cikakken Bayani Ne Akan Irin Matsalar Dake Tattare Da Amfani Da Wasu Whatsapp Wadanda Babu Su A Manhajar Playstore.

Wadannan Apps Ko Ince Whatsapp Wanda A Yanzu Sun Zama Ruwan Dare Sabo Da Wasu Fasahohi Da Aka Kara Musu Fiye Da Wancan Whasapp Din Na Ainishi Wanda Muke Amfani Dashi.

To Maganar Gaskiya Duk Wani Whatsapp Da Zakayi Amfani Dashi Bayan Wancan Na Farko Wanda Muke Amfani Dashi Ne.

Dalili Shine Shi Wannan Whatsapp Da Muke Using Dashi A Baya Shine Application Mai Register.

Minene Application Mai Register ? Kuma Dama Anawa Application Register ?.

Application Mai Register Tamkar Yaro Ne A Lokacin Da Aka Kaishi Makaranta Kaga Babu Yadda Za,ayi Wani Yaron Yasa Kansa Kai Tsaye Zuwa Makaranta Batare Da An Kaishi Kuma Anmar Register A Matsayin Dalilbi Ba.

Kaga Kenan Duk Wanda Yaje Makaranta To Yana Da Register Kuma Malumai Sun Yadda Dashi Kuma Sunyi Imanin Cewar Duk Abinda Yafaru Dashi A Wannan Lokaci To Nauyinsa Ya Rataya Ne A Wuyansu.

To Duba Da Haka Yasa Shi Kansa Application Ake Mar Register Yadda Shi Wannan Wanda Yayi Wannan Application Zai Bada Duk Wani Bayanai Nasa Tare Da Bada Tabbacin Cewar Bazai Ha,inci Wani Daga Cikin Masu Amfani Da Wannan Application Ba.

Tambaya Ta Biyu Itace, Eh Anawa Application Register Kamar Yadda Akewa Kungiya Ko Wani Company Register.

Ita Wannan Register Google Ne Da Kansa Yakewa Applications Register Wanda Indai Kaga Babu Application A Cikin Playstore To Wannan Application Yana Da Wata Matsala Daga Wajen Wanda Yayi Shi.

Misalan Irin Wadannan Whatsapp Da Applications Wadanda Basu Da Register Sun Hada… Gb Whatsapp, Nigerian Whasapp, Adwhatsapp, Senegal Whatsapp, Vidmate, Kai Da Dai Sauransu.

Akwai Applications Masu Yawa Wadanda Suke Da Matsala Wanda Playstore Yaki Karbansu, Wasu Kuma Saboda Matsalar Da App Din Nasu Keda Shi Yahana Su Bawa Google Yamusu Register.

Misali Ka Gwada Rubuta Sunan Daya Daga Cikin Wadannan Applications Da Muka Ajiye Muku Sunansu Zakuga Babu Ko Daya A Manhajar Google Playstore.

Amma Idan Kayi Searching Na Whatsapp Kawai Ko Whatsapp Business To Wadannan Zaka Gansu Saboda Yardaddu Ne An Musu Register.

Yin Amfani Da Wadannan Whatsapp Guda Biyu Sune Kwanciyar Hankalin Duk Wani Maiyin Whatsapp, Domin Idan Baka Samu Matsala Yanzu Ba To Anan Gaba Zasu Baka Wannan Matsalar Ko Ba,a Dade Ko Ba,a Jimaba.

Amfani Da Gb Whatsapp Ko Adwhatsapp Kai Koma Dai Wane Irin Whatsapp Ne Matukar Ba Daya Daga Cikin Wadannan Biyun Da Muka Lissafo Ba, Zai Iya Sama Sanadin Da Wata Rana Zasu Nadi Bayanan Kan Sim Dinka.

Misali Idan Kana Save Din Bvn Ko Pin Dinka Wanda Kake Amfani Dashi A Account Dinka To Zasu Iya Sambadar Bayananka Su Tasheka Sarai.

Sannan Ko Haka Bata Faruba To Zasuna Banning Na Number Din Wayarka Lokaci Zuwa Lokaci Sakamakon Amfani Da Kakeyi Da Wannan Whatsapp Din Wanda Ba,a Yadda Dashi Ba.

To Masu Saurare Kundai Ji Dan Bayanin Da Muka Kawo Muku A Takaice Dangane Da Irin Hanyoyin Da Yakamata Kubi Domin Kare Account Da Dukiyarku Daga Yan Iska.

Advertisement

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Advertisement
Back to top button
error: Alert: Content selection is disabled!!