Yadda Zaka Bude Gmail Address Kamar Guda Goma ( 10 ) Da Kanka Batare Da Kasa Phone Number Din Wayarka Ba.
Yadda Zaka Bude Gmail Address Kamar Guda Goma ( 10 ) Da Kanka Batare Da Kasa Phone Number Din Wayarka Ba.
Jama,a Assalamu Alaikum Barkanmu Da Warhaka Sannunmu Da Sake Saduwa Daku A Wannan Shafi Namu Mai Albarka Hikimatv.
A Cikin Posting Din Namu Nayau Zamu Kawo Muku Cikakken Bayani Akan Yadda Zaka Bude Sabon Gmail Account Ba Tare Da Kayi Amfani Da Phone Number Ba.
Abinda Muke Bukata Shine Ka Karanta Wannan Bayani Daki-daki Kuma Dalla-dalla, Sannan Ka Karanta Wannan Bayani Tun Daga Farko Har Karshe Domin Fahimtar Yadda Abin Yake.
To Da Farko Dai Kowa Yasan Cewar Mafi Yawan Wayoyinmu Na Android Suna Suwa Da Gmail App.
Sannan Idanma Wayarka Batazo Da Gmail App Ba, To Zaka Iya Daukowa App Din A Google.
Sannan Zaka Iya Shiga Ta Setting Na Application Ka Shiga Wurin Da Aka Rubuta Account, Bayan Nan Saika Danna Wurin Da Aka Rubuta Google, Daga Nan Saika Saka Fingerprint Dinka Ko Password Din Wayarka.
To Daga Nan Zai Kawo Ka Shafi Na Gaba Inda Anan Saika Duba Zakaga Wurin Da Aka Rubuta Create Account, Bayan Ka Danna Wannan Zasu Tambayeka Nakane Account Din Ko Na Kasuwanci Ne, To Anan Saika Dauki Ko Ka Danna For Myself, To Daga Nan Zasu Tiraka Izuwa Shafi Na Gaba Wanda Zaka Cike Sunanka Na Farko Da Sunanka Na Biyu.
Bayan Ka Cike Sunanka Zasu Kaika Izuwa Shafi Na Gaba, To Zaka Cike Watan Haihuwarka Da Shekarunka, Da Ranar Da Aka Haifeka Wato A Turance, Day, Month, Then Year.
To Bayan Ka Cike Wannan Wuri Zaka Danna Next, Bayan Ka Danna Next Zasu Turaka Izuwa Shafi Na Gaba Inda Anan Kuma Zakaga Wurin Da Aka Rubuta Kazabi Sunan Gmail Din Da Kake So.
Misali kano@gmail.com Sunan Zai Kasance Kamar Haka, To Bayan Kazaba, Daga Nan Zaka Matsa Zuwa Wurin Da Zaka Zabi Password, Wato Numbobi Na Tsaro, Zaka Iya Saka Phone Number Din Wayarka Domin Gudun Kadda Ka Manta.
To A Step Wato Mataki Na Biyun Karshe Shine Wanda Muke Bayani Akansa Shine Wanda Zaka Saka Phone Number Din Wayarka, To Madadin Kasa Phone Number Din Sai Ka Duba Kasa Daga Hannun Hagu Can Kasa Zakaga Wurin Da Aka Rubuta Skip, Wato Ka Tsallake Wannan Mataki A Turance, To Saika Danna Wannan Wurin Da Aka Rubuta Skip Din To Daga Nan.
Sai Step Na Karshe Wanda Anan Ne Zaka Danna Next To Daga Nan Ka Gama Bude Sabon Gmail Batare Da Phone Number Ba, Haka Zakayi Tayi Idan Kanason Bude Wasu Gmail Din.
Amma Kana Iya Zuwa Wannan Wuri Na Saka Phone Number Dinka Kaga Babu Wannan Wuri Da Aka Rubuta Skip, To Idan Haka Ta Kasance Saika Saka Phone Number Dinka Ka Kara Bude Wani Da Ita Kadda Ka Damu Zaka Iya Bude Gmail Kamar Guda Biyar Da Phone Number Daya.
Mungode Mungode Dukka Dukka Anan Muka Kawo Karshen Wannan Darasi Inda Muke Fatan Zaku Kasance Da Wannan Shafi Namu Mai Suna Hikimatv Domin Samun Sababbin Shirye-shiryenmu Akowane Lokaci.