Yadda Zaka Gane Idan Wani Yana Ganin Chat dinka Na Whatsapp
Jama’a Assalamu alaikum warahamatullah barkanmu da sake kasancewa daku a wannan shafin namu mai Albarka Hikimatv.
Kamar de yadda kuka sani whatsapp na daya daga cikin abubuwan da akafi amfani fasu musamman wajen chat, hira, video call, kasuwanci da sauransu.
Kasancewar yan mata da samari suna ta amfani dashi, hakanne yasa wasu daga cikin samarin ko yan matan suke leqen asiri na abun da dayansu yakeyi a whatsapp din, wanda idan suka hada hanyar leqen asirin a wayar da sukeso su gano abun da sukeyi din, Zasu dinga ganin chat, contact, kome nasu zasu iya gani.
Domin ganewa ko wani yana maka leqen asiri a whatsapp dinka ga yadda zakayi:
Da farko ka shiga whatsapp dinka saila taba alamar … ta gefan dama
Sannan saika shiga Linked Devices
Daka shiga idan har ana maka leqen asiri zakaga jerin abubuwan da ake leqen asirin naka, kamar de yadda yake ajikin hoton na kasa
Idan kaga wannan abun to tabbas akwai wanda yake maka leqen asiri yake ganin dukkan abubuwan da kakeyi ko kikeyi a whatsapp din ka.
Dan haka idan kaga irin haka saika danna akan abun daka gani saika shiga LogOut kamar haka
daga nan bayan ka danna zatayi processing sannan zata saukema dukkan wanda yayi link din wayarsa da taka yakr ganin sirrin ka.
Shikkenan idan har kaga wajen kamar haka shikkenan babu wanda yake ganin sirrin ka.
Allah ya bada sa a