Tutorials

Yadda Zaka Samu Kudi Ta Hanyar Dora Wakoki Koda Kai Ba Mawaki Bane Ta Hanyar Amfani Da Audiomack.

Advertisement Join Our Whatsapp Group

Jama,a Assalamu Alaikum Warahamatullahi Wabarakatuhu, barkanmu Da Sake Saduwa Daku A Cikin Wannan Shafi Namu Mai Albarka Hikimatv.

A Cikin Kunshin Sakon Ko Garabasar Dazamu Muku Bayani Ayau, zamu Kawo Muku Bayani Ne Akan Wata Hanya Dazakabi Wurin Dora Wakoki Ko Wani Audio Na Labari Da Kake Karantawa Ko Wasu Wakoki Da Kake Tunanin Maisu Baya Dorawa.

To Anan Zaka Iya Dora Wadannan Wakoki Ko Labarai Akan Wannan Man Haja Ta Audiomack Domin Fara Samun Kudi, Abin Babu Wata Wahala Domin Sanin Yadda Zakayi Muje Cikin Bayanin Kai Tsaye.

Amma Ka Tabbatar Dacewar Ka Karanta Wannan Bayani A Nutse Kafin Ka Fara Wannan Aiki Sannan Zamu Ajiye Muku Link Din Wannan Application Mai Suna Audiomack Dakuma Creators.

Zamu Muku Cikakken Bayani Akan Audiomack Dakuma Creator.

Da Farko Dai Shi Audiomack Wani Application Ne Ko Muce Manhaja Da Ake Sauraren Wakoki, Misali Player Ce Kamar Music Player Dake Kan Wayarka Ko Kuma Boomplay Takan Wayarka, Ita Wannan Player Zaka Iya Sauraren Wakoki Akanta Kamar Yadda Kake Sauraro Takan Player Din Dake Kan Wayarka.

Sai Dai Banbancin Dake Tsakaninsu Shine, Ita Wannan Player Mai Suna Audiomack Ana Sauraren Wakoki Ne Akanta Matukar Kana Da Data Ka Kuna Datar Kan Wayarka, Sannan Zaka Iya Suraren Wakokinka Koda Baka Kunna Databa Saboda Wadannan Nakane, Amma Matukar Baka Saukar Dasu Izuwa Kan Wayarkaba To Saika Kunna Data Zaka Saurari Ko Kayi Download Na Wadannan Wakoki.

Shi Wannan Application Mai Suna Audiomack Yana Dauke Da Wakokin Da Hausawa Ke Rerawa Tare Da Wadanda Turawa Da Yan Kudu Ke Rerawa Zaka Iya Searching Na Kowace Waka Ta Hanyar Rubuta Sunan Wakar A Wurin Searching.

Wannan Kenan Yanzu Zamu Kawo Muku Bayani Akan Creator Domin Saidashi Ne Zaka Iya Upload Na Waka Izuwa Kan Wannan Application Mai Suna Audiomack.

Sannan Wani Abun Birgewa Dangane Da Wannan Application Shine Koda Bakayi Share Ba Zaka Iya Samun Views Amma Yin Share Din Zai Kara Maka Samun Views.

Creator, Creator Dai Wani Application Ne Wanda Duk Wani Wanda Zaiyi Wannan Harkar Ta Amfani Da Audiomack To Dole Ne Yayi Download Dinsa.

Shima Wannan Application Zakayi Register Ne Ta Cikinsa Ta Hanyar Dora Gmail Account Dinka Dakuma Password, A Sauwakema Zaka Iya Register Da Irin Details Din Dakayi Register Dashi A Audiomack.

Bayan Kayi Download Na Wadannan Applications Guda Biyu Saika Bude Na Farko Wato Audiomack Idan Ka Budeshi Zakaga Wurin Da Aka Rubuta Sign Up Saika Danna Daga Nan Zaka Cike Full Sunanka Da Number Din Wayarka Da Gmail Dinka Daga Nan Zasu Turoma Cods Takan Number Din Wayarka Kota Kan Gmail Dinka.

Zaka Saka Wadannan Numbobi Da Aka Turoma Daga Nan Zaice Kayi Register Successfully Daga Nan Saika Sauka Kahau Wancan Application Din Na Biyu Mai Suna Creator Kana Shiga Saika Danna Wurin Register Kasa Gmail Dinka Kasa Password Zaka Iya Maimaita Wanda Kayi Register Dashi Na Audiomack.

Daga Nan Zakaga Wurin Wata Kibiya Wanda Idan Ka Danna Zai Baka Damar Upload To Bayan Ka Taba Zai Kaika Shafi Na Gaba Anan Ma Zakaga Wani Wurin Yace Upload Song Wato Ka Dauko Wakar Da Kakeson Dorawa.

To Bayan Ka Kara Danna Wannan Wurin Zai Kaika Cikin File manager Din Kan Wayarka Saika Zabi Wakar Da Kakeson Dorawa Ka Danna Upload Nan Take Zatayi Upload Tabaka Damar Rubuta Sunan Mawakin Da Sunan Wakar Da Kalar Wakar Da Hoton Wakar Da Bayani Akan Wakar Da Dau Sauran Bayanan Da Suka Shafi Wannan Waka.

To Bayan Ka Cike Komai Saika Danna Next Haka Zakayi Ta Danna Next Har Wakar Tahau Kan Wannan Application Anan Zakaga Wannan Wakar Kuma Zakaga Mutanen Da Suke Kallon Wannan Waka.

Zasu Fara Biyanka Ne Bayan Kadora Wakoki Adadin Yadda Sukeso Ko Kuma Kasamu Views Adadin Yadda Sukeso.

Sannan Zaka Iya Dora Karatu Ko Wani Labari Da Kake Karantawa Ba Dole Sai Wakaba, Sannan Zaka Iya Dora Wakokin Wani Matukar Ka Tabbatar Dacewar Mai Wakokin Baya Dorawasu.

Sannan Zaka Iya Seaching A Youtube Na Yadda Ake Samun Kudi Ta Hanyar Amfani Da Audiomack To Anan Zaka Iya Kallon Videon Yadda Ake Komai Da Komai.

Wannan Shawara Ce Idan Baka Fahimci Wani Wajen A Wannan Bayani Dana Kawoma Ba.

Ga Link Din Audiomack Saiku Danna Wurin Da Aka Rubuta “Download Audiomack Now”

Download Audiomack Now

Wannan Kuma Shine Link Din Creator Saika Danna Wurin Da Aka Rubuta Download “Creator Now “

Download Creator Now

Advertisement

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Advertisement
Back to top button
error: Alert: Content selection is disabled!!