Tutorials

Yadda Zaka Gano Application Din Da Suke Chinyema Space Din Kan Wayarka ( Phone Memory ).

Advertisement Join Our Whatsapp Group

Jama,a Assalamu Alaikum Barkanku Da Shigowa Cikin Wannan Shafi Namu Mai Abarka Hikimatv.

A Cikin Wannan Posting Namu Nayau Zamu Kawo Muku Cikakken Bayani Akan Yadda Zakasan Dukkan Application Din Da Suke Cinyema Space Na Wayarka Dakuma Ma Irin Wayar Daya Kamata Kasaya.

Mutane da dama suna sayan wayoyin dake da karancin space nakan waya wato ( phone memory ) a turance.

To gareku mabiyan wannan site namu, idan da hali a shawace yana da kyau kasamu wayar da space dinta yakai 16Gb Ko 32 Gb A babu domin idan kasayi waya wadda take da space kasa da 16Gb Ko 32Gb to kadinga samun matsala da wannan wayar domin space din kan wayarka yadinga ma warning.

Saboda haka a shawarce kuma a takaice yana da kyau kanemi waya mai space domin kaji dadin amfani da ita anan gaba.

Wannan kenan dangane da wayar daya kamata kasaya domin gujewa irin wannan matsalar ta rashin space.

To bari mukoma bangaren yadda zaka gane application din da suke jamaka space acikin wayarka.

Da farko dai abinda zakayi la,akari dashi shine wane application ne kafiye amfani dashi yau da gobe ?

Sannan wanne application ne yake da nauyi ko yake baka matsala idan kana amfani dashi ?

Idan kayi wannan tunani to zaka iya yankewa kanka shawara batare da bata wani lokaci ba, domin mutane da dama suna korafi akan wayarsu tana ta nuna musu cewar babu space.

To da farko dai idan yakasance wayarka bata da space mai yawa kamar yadda nayi bayani a baya.

Misali wayarka space dinta baifi 16Gb Ko 8Gb Ko 4Gb Ba to ko shakka babu idan har kana yawan installing na Application zaka rika fadawa cikin wannan matsala ta insuffient space.

A shawarce idan kai mai yawan son installing na application ne to kasamu waya mai 32Gb Ko 64Gb domin gujewa wannan matsala.

Domin kuwa idan har wayarka bata da space na kirki to wadannan application da kake installing su zasu rika cinyema space din kan wayanka.

Ga jerin irin application din da suke yawan cin space din kan waya idan ana yawan amfani dasu.

1- Whatsapp.

2- Youtube.

3-Chrome Browser.

4- Uc Browser.

5- Youtube.

6- Facebook.

7- Kinemaster.

8- Opera Mini.

9- Games.

10- Vidmate.

Da dai sauransu to wadannan applications da wasu wadanda ban lissafo ba amma kai kana iya saninsu saboda kai kale amfani dasu zaka iya dubasu ta wannan hanya da zamu muku bayani anan gaba kadan.

Domin kusan wanne application ne yake cinye muku space din kan wayoyinku batare da kunsani ba.

Abinda yakamata ku sani shine idan kasan kana amfani da application to kadda kayi clear data dinsa kamar yadda zamu muku bayani domin idan kayi clear data dinsa to idan game ne ko wani application ne da kakeyin wani abu yake saving to zai dawo dakai farko ne.

To kaga kuwa babu damar kayi clear data dinsa, sai dai kayi clear data na wanda kasan baka amfani dashi amma yana cin space din kan wayarka wannan zaka iyayin clear data dinsa.

Da farko idan zakayi clear datar ko ince kanaso kasan wannan applocation din yana cin space din kan wayarka ko baya ci.

Saika danne wannan application kamar zaka gogeshi, daga nan zai baka option da yawa irinsu ” Share, Uninstall, App Infor Da Send To Desctop.

To anan saika danna kan App Info daga nan zaikaika wurin da zakaga Storage and Catches, saika danna wannan wurin daga nan zakaga space din da wannan application din yaja.

Sannan zakaga wurin da zakayi clear data dinsa.

Mungode mungode mungode saimun hadu daku a posting na gaba sannan kadda ku manta da danna alamar allow na notification domin samun sababbin shirye-shiryenmu.

Advertisement

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Advertisement
Back to top button
error: Alert: Content selection is disabled!!