Yadda Zaka Ragewa Video Nauyi Daga Data Zuwa Mp4 Batare Daya Ragewa Videon Clear Ba.
Jama,a assalamu alaikum barkanmu da sake saduwa daku A cikin wannan shafi namu mai suna Hilimatv.
A cikin wannan bayani da zamu kawo muku zamu muku cikakken bayani akan yadda zaku maida video data zuwa mp4 cikin sauki.
Saiku karanta wannan bayani tun daga farko har karshe domin sanin yadda zakuyi wannan aiki.
Da farko ana bukatar yakasance kana da gmail account, sannan yakasance ka dorashi akan wayanka, dama ta biyu itace idan baka da gmail to yakasance wayarka tana da opera mini ko chrome ko uc browser.
Idan yakasance kana da gmail to saika dorashi akan wayanka sannan ka nemi playstore application saika hau kansa bayan kahau saika rubuta video converter, anan zasu bakasu da dama, saidai ba kowacce ce mai kyau ba.
To wannan ya rage gareka ka zabi wadda kake so, idan kuma baka da gmail account to saika hau kan google chrome ko uc browser ko opera mini.
Bayan kahau saikayi searching na video converter saika shiga daya daga cikin site din da suka baka kayi download dinta.
Amma domin mu saukaka muku kadda kuje ku dauko wadda take da matsala zamu ajiye muku link din dazaku danna domin saukar da ita wannan wadda muka yadda da ita.
To kafin mu ajiye muku link din bari mu muku bayani akan yadda zakuyi converting din videon daga data zuwa mp4 Ko 3gp saiku biyomu kai tsaye.
To da farko bayan ka saukar da wannan application mai suna To Mp4 Video Converter, Saika danna kan wannan application din daga nan zai kaika cikinsa.
Anan Zakaga Select saika danna kan select din daga nan zai watso maka dukkanin videon dake kan wayarka to saika zabi videon da kake son ka maidata mp4 saika danna kanta daga nan zai baka damar kazabi mp4 Ko 3gp zaka maida videon.
Kana ganin haka saika danna kan mp4 idan mp4 zaka maidashi idan kuma 3gp zaka maidashi to saika taba kan 3gp.
Yauwa ga link din application din saiku danna kansa domin saukar dashi zuwa kan wayoyinku.
Download Mp4 Video Converter Now
Mungode mungode mungode kadda ku manta da kasancewa da wannan site namu domin samun sababbin shirye-shiryenmu akowane lokaci.