Yadda Zaka Ragewa Wayarka Ta Android Shan Data Da Kuma Chaji Batare Da Kayi Amfani Da Wani Application Ba.
A Darasin Namu Nayau Wanda Zamu Kawo Muku Cikakken Bayani Akan Yadda Zaka Ragewa Wayarka Shan Data Da Kuma Chaji Saiku Karanta Cikakken Bayanin Da Zamu Kawo Muku.
Sannan Muna Masu Neman Alfarma Daga Gareku Na Danna Mana Alamar Notification Da Kuke Gani Tana Cewa Allow To Saiku Danna Allow Din Domin Ta Hakane Kawai Zakuna Samun Sako Idan Munsaki Wani Sabon Posting.
To Bari Mu Fara Kawo Muku Bayani Akan Hanyoyin Dazakubi Domin Yin Maganin Wannan Matsala Ta Yawan Shan Data Da Chaji Da Wayarku Takeyi.
Bari Mu Fara Da Matsalar Shan Data Tunda Ita Muka Kara Ambata A Title Din Posting Din Namu.
1_ Matsalar Shan Data.
Matsalar Shan Data Na Matukar Ciwa Mutane Tuwo A Kwarya Domin Muddin Mutum Yana Browsing To Dole Wannan Matsala Ta Zamemar Alaka Kai Kasancewar Yanzu A Halin Da Duk Wani Dan Nigeria Yake Ciki Yasan Irin Yadda Data Ke Karewa Da Wuri Batare Da Wani Bata Lokaci Ba.
Wannan Dai Wani Sabon Iskanci Ne Da Zalunci Da MTN Suka Fito Dashi, Amma A Wani Bangaren Za,a Iya Cewa Matsalar Kamfanin Wayoyi Ne.
Miyasa Akace Laifin Kamfanin Wayoyi Ne ?
Amsa, Yanzu Mafi Yawancin Wayoyin Da Kamfanin Sukeyi Wayoyi Ne Masu Ram Da 4G Network.
Ram Da 4G Network Suna Taka Muhimmiyar Rawa Wajen Janye Data Da Shan Chaji Na Kowace Irin Waya Ta Android.
Ram Dai Kamar Yadda Kuka Sani Shine Kwakwalwar Waya Shiyake Taimakawa Waya Wurin Saurin Yin Abubuwan Da Aka Umarceta Duk Wayar Da Bata Da 2, 3, 4 Ko 6 Ram To Wannan Wayar Sai, a Hankali.
Saboda Haka Duk Wayar Da Ram Dinta Baifi 2Gb Ram Ko 4Gb Ram Ba To Wannan Wayar Bazata Sha Chaji Ko Shan Data Ba.
Idan Wayarka Tana Da Babban Ram Kamar 4Gb Ko 6Gb Ko 8Gb To Abinda Yakamata Kayi Domin Ragewa Wannan Waya Shan Data To Ka Shiga Setting Din Wayar Ka Maida Network Dinta Zuwa 3G Only Idan A Akan 4G Yake To Yin Hakan Zaiyi Matukar Ragewa Wayarka Shan Data.
Wannan Kenan Dangane Da Matsalar Shan Data, Sai Dai Maida Network Din Wayarka Zuwa 3G Zai Rage Mata Saurin Browsing.
A Daya Bangaren Kuma Idan Kana So Ka Ragewa Wayarka Shan Chaji To Abinda Yakamata Kayi Da Farko Shine Kana Ragewa Wayarka Hasken Screen Domin Idan Ka Dauke Kira Babu Abunda Yafi Hasken Screen Shan Chaji A Wayar Android.
Bin Wannan Hanya Always Zaiyi Matukar Taimako A Gareka, Sannan Zaka Iya Kunna Eye Care Shima Yana Kare Ido Daga Fadawa Masifar Hasken Screen.
Sannan Idan Ka Bude Eye Care Zakaga Hasken Wayar Ya Sanja Daga Fari Zuwa Ja, To Wannan Shima Yana Ragewa Waya Shan Chaji.
Wannan Dai Sune Atakaice Hanyoyi Biyu Dazakabi Domin Ragewa Wayarka Ta Android Shan Data Dakuma Chaji Batare Da Kayi Amfani Da Wani Application Ba.
Mungode ! Mungode !! Mungode !!! Kadda Ku Manta Da Kasancewa Da Wannan Blog Namu Domin Samun Dukkan Abubuwan Da Suka Danganci Wayoyin Android.