Yadda Zaka Gyara Katin Zaben ka wato Voter’s Card da Kanka
Assalamu Alaikum Jama’a Barkanmu da sake kasancewa daku a wannan shafin namu mai Albarka Na HikimaTv
Kamar de yadda kuka sani Hukumar zabe ta kasa wato INEC ta fitar da hanyar da zakuyi gyaran katin zabenku da kanku ta hanyar amfani da wayoyon ku.
Tun a shekarar 2021 de hukumar ta bude shafin nata domin bawa masu sha,awar yin sabon katin zabe kokuma gyara ko chanja mazaba, wanda tun a lokacin mutane dayawa sukayi ta kokarin yi, har aka kai ga wasu daga ciki sun mallaki nasu.
A ranar 30 ga watan May na 2022 hukumar ta rufe bada damar yin sabon katin zaben, amma kuma bata rufe sauran abubuwan ba,
A yanzu haka idan gyara ne dakai zaka iyayi amma ba zaka iya sabuwar Register ba sabo da an rufe.
Ga Abubuwan da zaka iyayi a yanzu haka:
- Review
- Tranafers
- Information update
- Collect your pvc
- Lost or Damage pvc
Review: Shine Idan kun yi rajista kuma har yanzu ba ku sake nazarin bayananku ba ta hanyar samar da hoton ku akan layi akan wannan dandali,
Transfer: amfaninsa shine Idan kun yi rajista kuma kuna son canza wurin kada kuri’a zuwa wata rumbun zabe,
Information update: idan kun yi rajista kuma kuna son sabunta ko gyara bayanan da ke kan Katin Zaɓenku
Collect your pvc: Idan kun yi rajista a baya kuma ba ku sami katin Zaɓen ku ba
Lost or Damage pvc: Idan kun rasa katin zabenku ko kuma idan PVC ɗinku ta lalace kuma kuna son maye gurbinsa
Danna Link din dake kasa domin Gyarawa
Shigo Nan domin Gyarawa
Allah ya bada sa’a