Yadda Ake Gane Original ( Wato Ainishin ) Space Da Ram Na Kowace Irin Wayar Android A Shekarar 2022.
Yadda Ake Gane Original ( Wato Ainishin ) Space Da Ram Na Kowace Irin Wayar Android A Shekarar 2022.
Jama,a Assalamu Alaikum Barkanmu Da Wannan Lokaci Sannunmu Da Sake Saduwa Daku A Cikin Wani Sabon Shiri Mai Suna Kimiyya Da Fasaha.
Acikin Shirin Namu Nayau Zamu Kawo Muku Cikakken Bayani Akan Yadda Ko Hanyar Dazakabi Ka Gane Ainishin Ram Da Space Na Ko Wace Irin Wayar Android.
Menene Space ?.
Space Dai Shine Adadin Megabite Da Waya Take Dashi,misali Zakaji Ance Wata Wayar Tana Da 16GB, Wata Tana Da 32GB, Wata Tana Da 64GB, Wata Tana Da 128GB Wata Kuma Tana Da 256GB, Kai Da Dai Sauransu To Wannan Space Din Shi Zai Taimakama Idan Kanason Dora Videos Ko Wakoki Da Yawa Adadin Space Din Wayarka Adadin Abinda Zaka Dora Akan Wayarka Saboda Haka Saika Kula Wajen Sayen Waya Domin Yanzu Zaka Iya Ganin Waya Tana Da 32Gb Nan Kuwa 16GB Ne To Akwai Hanyar Dazakabi Idan Kanason Sanin Takamaiman Ko Ince Hakikanin Space Din Wayar Dazaka Saya.
Menene Ram ?.
Ram Shine Random Access Memory.
Shi Wannan Abu Yana Taimakwa Wayane Wajen Amfani, Misali Sauri Idan Kana Amfani Da Ita, Rashin Kamewa, Saurin Browsing Da Dai Sauran Abubuwa To Kaga Kuwa Yana Da Kyau Ka Sayi Wayar Da Take Da Wannan Abu Babba Idan Har Bakaso Wayarka Ta Rika Kamewa Ko Yazama Bata Saurin Browsing Akan Lokaci Ko Abinda Zaka Dauko Yana Daukanka Tsawon Wani Lokaci.
To Bari Mu Muku Cikakken Bayani Akan Hanyar Da Zakubi Domin Gano Hakikanin Space Da Ram Na Gaskiya Kafin Ku Sayi Waya Saboda Kadda Rashin Sani Yasa A Kwantar Daku.
Da Farko Idan Ka Karbi Wayar Da Zaka Saya Saika Shiga Cikin Ko Kan Zander Kai Tsaye Kadda Ka Shiga Setting Domin Shi Duba Space Ko Ram Takan Zander Shadanci Ne, Bayan Ka Shiga Kan Zander Saika Ja Zuwa Chan Gefe Zakaga Wurin Da Aka Rubuta File To Anan Zakaga Space Din Wayar Duk Abinda Ta Nunama Tanan To Shine Hakikanin Space Na Wayar Saboda Ita Zander Ba,a Mata Karya.
To Idan Kaga Space Din Wayar 10GB Ko 12GB Ne To Suna Nufin 16GB Ne To Kaga Wayarka Ram Dinta 1GB Ne, Idan Kuma Space Dinta Kaga 23GB Ko 25GB To Ram Dinta Zai Iya Kasancewa 2GB KO 3GB, Idan Kuma Space Dinta Yakasance 52GB Ko 64GB Ne To Ram Dinta Zai Kasance 4GB KO 6GB Ne, Idan Kuma Space Yakasance 123GB Ko 125GB Ne To Wayar Zata Iya Kasancewa Ram Dinta 6GB Ko 8GB Ne, Idan Kuma Space Dinta Ya Kasance 245GB Ko 256GB Ne To Ram Dinta Zai Kasance Kai Tsaye 8GB Ne To Wannan Dai Shine Takaitaccen Hanyar Dazakabi Domin Gane Ram Da Space Na Ainishi Ba Copy Ba.
Dafatan Kunji Dadin Wannan Bayani Inda Muke Fatan Zaku Ajiye Mana Comment Na Godiya Tare Da Share Na Wannan Post Namu Domin Wasu Suma Su Karu Mungode.