Tutorials

Yadda Zaka Boye Komi A Wayarka Duk Duniya Babu Mai Ganinsa Batare Da Kayi Amfani Da Wani Application Ba.

Advertisement Join Our Whatsapp Group

Jama,a Assalamu Alaikum Barkanmu Da Wannan Lokaci, sannunmu Da Sake Saduwa Daku A Cikin Wani Sabon Post.

A Posting Din Namu Nayau Zamu Kawo Muku Cikakken Bayani Akan Yadda Zaka Boye Wasu Abubuwa A Cikin Wayarka Batare Da Kayi Download Na Kowane Application Ba.

Menene Zan Iya Boyewa ? Kuma Menene Bazan Iya Boyewa Ba ?.

Amsa :

Zaka Iya Boye Wakokin Da Kake Da Bukata.
Sannan Zaka Iya Boye Hotunan Da Kake Bukata.
Har Ila Yau Zaka Iya Boye Video Ko Folder Ma Gaba Daya Batare Da Kuma Kayi Amfani Da App Ba Kamar Yadda Muka Yi Muku Bayani.

Ku Biyo Mu Domin Jin Yadda Zakuyi Abin Mai Sauki Ne Babu Wata Wahala A Tattare Dashi.

Da Farko Dai Zaka Shiga Kan File Manager Na Wayarka Bari Mu Fara Daga Kan Folder,Idan Ka Shiga Cikin File Manager Saika Zabi Folder Din Dakake Son Ka Boye Wanda Bakason Kowa Ya Ganta Wata Kila Saboda Wasu Videos Ko Hotuna Ko Wakoki Daka Ajiye Ne Yasa Bakaso Kowa Ya Ganta.

Bayan Kaje Dai Dai Kan Wannan Folder Saika Danneta,Zata Baka Wasu Alamu Daga Kasa Irinsu CUT, RENAME, PAST, Da Dai Sauransu To Zaka Taba Wurin Da Aka Rubuta Rename Ne Daga Nan Saika Taba Alamar Abin Rubutun Nan Dayake Motsi Daga Nan Saika Dawo Dashi Farkon Sunan Folder Din Bari Na Muku Misali.

Misali Sunan Folder Din Danayi Shine ” My Folder” To Idan Ka Danne Kan My Folder Kataba Wurin Da Aka Rubuta Rename Saika Maida Sunan Kamar Haka ( .My Folder ) Amma Banda Wannan Bracket Din Dana Saka Daga Nan Saika Danna Ok.

To Daga Nan Zasuce Maka Wannan Folder Zata Bace Kuma Babu Mai Ganinta Saika Danna Ok Ka Yarda Daga Nan Wannan Folder Zata Bace.

To Haka Zakayi Idanma Wata Video Ce Ko Waka Ko Hoto Guda Daya.

Idan Kuma Kanaso Ka Fito Da Wannan Folder To Zaka Koma File Manager Saika Taba Wurin Da Akayi Wata Alama Ta … Guda Uku A Tsaye Ko A Kwance Idan Kataba Wannan Wuri Zakaga Inda Aka Rubuta Show Ko Show Hiding Files, Wato A Nunama Abinda Aka Boye Daga Nan Wannan Folder Ko Videos Ko Hotuna Ko Wakoki Zasu Fito To Saika Danne Folder Din Ko Videon Ko Hoton Ka Dada Taba Wurin Rename Saika Cire Wannan . Din Shikenan Saikayi Ok.

Take Wannan Video Zai Dawo Kan Wayarka Kuma Zaka Iya Yin Play Dinsa Amma Indai Ba,a Cire Wannan . Dinba To Koda Ka Dannashi Bazaiyi Play Ba Zai Zamane Kamar Virus.

Dafatan Kun Gane Wannan Bayani Namu Idan Kuma Baku Ganeba To Zaku Iya Ajiye Comment Domin Muyi Muku Video Ku Kalla Dalla-dalla.

Mungode – Mungode Kadda Ku Manta Dayin Like, Subscribe, Comment Domin Samun Sababbin Shirye-shiryenmu Akowane Lokaci Mungode.

Advertisement

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Advertisement
Back to top button
error: Alert: Content selection is disabled!!