Yadda Zakayi Download na Youtube Video ta Telegram
Assalamu alaikum barkanmu da wannan lokaci sannunmu da sake kasancewa daku a wannan shafin namu mai Albarka hikimatv.
A yau zanyi muku bayani akan yadda zakuyi download na bidiyon youtube ta hanyar amfani da telegram.
Kamar de yadda kuka sani youtube basu bada damar a sauke video kai tsaye daga youtube ba, saide ta hanyar amfani da wasu application din, wanda hakan yana batawa wasu rai kasancewa basajin dadin download da wasu app din.
To a yanzu ga wata hanya wacce zakuyi amfani da telegram dinku domin kuyi download na videon youtube cikin sauki.
Domin sauke videon youtube ta hanyar telegram, saiku shiga link din da yake kasa
Youtube video On Telegram
Idan kun shiga link din zai kaiku telegram to sai kuje youtube kuyi copy na link din videon da kukeso kuyi download sai kuyi copy kuzo wannan link din da kuka shiga kuyi post na link din, saiku tura, anan take zakuga ya baku damar download.
Allah ya bada sa’a