Yadda Zaka Ragewa Tiktok Shan Data
Assalamu alaikum Warahamatullah, Barkanku da sake kasancewa damu a wannan shafin namu mai Albarka.
A yau zanyi magana akan yadda zaku rage shan data a tiktok.
Kamar de yadda kuka sani tiktok, yana daya daga cikin platform wanda akafi amfani dashi, musamman samari da yan mata.
Kuma tiktok yana daya daga cikin abubuwan da sukafi bada nishadi, kasancewar video ake wallafawa a cikinsa, shiyasa yake da shan data.
Mutane sunaso suga suna amfani da tiktok kasancewa a yanzu shine kan gaba wajen bada nishadi a social media, saide kuma wasu suna kuka dashi domin shan datan da yake musu.
Shiyasa wasu suke hakura dashi, domin idan suka biya masa kullum sai sun batar da kudi wajen saya masa data.
Dan haka a wannan darasin zaku koyi yadda zaku rage masa shan data,
Ga yadda zakuyi:
Da farko ka shiga tiktok dinka, sannan saika shiga Profile dinka
Idan ya bude saika shiga alamar menu
Sannan saika shiga Settings and Privacy
Idan ya bude sai kayi chan kasa ka duba inda aka Rubuta Data Saver
Saika shiga Sannan ka kunna shi, idan kuma kaga a kunne yake to shikkenan saika barshi a haka
Shikkenan idan kayi wannan settings din to insha Allah tiktok dinka zai dena sha maka data.
Allah ya bada Sa’a