Idan Ka Hada Layin ka Da NIN Kuma har Yanzu Baka Iya Kira – Ga Abin da Zakayi
Assalamu Alaikuma Jama’a barkanmu da wannan lokaci da fatan kuna cikin koshin Lafiya.
Idan baku mantaba a Ranar Litinin 4 ga watan Afrilu 2022 Gwamnatin Tarayya ta umarci hukumar sadarwa dasu hana kowane layi fitar kira idan har ba’a hada shi da NIN number ba.
Yayin da hukumar sadarwar ta toshe Layuka sama da Miliyan 72.77 wadanda ba’a hadasu da nin number ba.
Sai de kuma duk da hakan wasu na korafin sun hade layin nasu da nin din amma hakan bai hana toshe musu layin nasu ba, dayawa sun hada da nin din amma kira da aika sako baya fita daga sim din nasu, sai de a kirasu kokuma a aiko musu sako kokuma suyi browsing da layin.
Sai de kuma daya daga cikin babban jami’an sadarwar ya lissafo wasu dalilai dake haddasa faruwar duk da ka hade sim dinka da nin amma kuma yakiyin kira
Ga Dalilan kamar haka:
- Rashin Yiwa layi Register da sunan da yake kan NIN din
- Matsalar Na’ura daga wajen hukumar
- Hada NIN da layuka da yawa
- Rashin kammala Register
- Matsalar Yanar Gizo
- Kuskuren yin abin da yakamata daga NIMC
Wadannan sune kadan daga cikin abubuwan da suke iya haddasa Rashin fitar kira duk da ka hade sim din naka da NIN.
Ga yadda Zaka magance matsalar idan ka hada sim dinka da NIN amma baya kira:
Abun da zakayi shine idan har ka tabbatar da ka hade sim dinka da nin amma kuma duk da hakan layin baya kira, to ka garzaya ofishin sadarwa na layin naka saika shigar musu da korafi akan hakan
Kamfanin sadarwar basuji dadin toshe layukan da akayiba, sabo da asarar kudin shiga da sukeyi dalilin faruwar hakan, Shiyasa idan ka shigar da korafin zasuyi gaggawar bibiya domin su magance maka matsalan naka.
A shawarce duk wanda ya fuskanci irin wannan matsalan to ya ziyarshi office din hukumar sadarwar na layin da yake amfani dashi ya shigar da korafi, Sukuma zasuyi kokarin rubuta wasika wa hukumar NIMC domin a magance matsalar.
Allah ya taimaka.