Tutorials

Yadda Zaka Ajiye Rubutu( Note) akan wayarka Koda ka chanja Waya zaka iya dawo dashi

Advertisement Join Our Whatsapp Group

Assalamu alaikum Warahamatullah barkanmu da sake kasancewa daku a wannan shafin namu mai Albarka hikimatv.

A yau nazo muku da bayani akan wani application mai matukar muhimmanci wanda zai taimaka muku wajen ajiye rubutunku akan waya, ta yanda koda kun chanja waya, kokuma wayan ta bata to zaka iya amfani dashi rubutunku ya dawo ba tare da wata matsalana.

Da farko ku ku shiga link dinnan ku sauke application din👇
Download App Here

Bayan kunyi download dinsa saiku budeshi, saiku danna wannan alamar icon na mutun din

Daga nan zai kawo muku inda zaku dora gmail dinku, saiku zabi gmail dinku wansa kukeso kuyi amfani dashi

Bayan kun zaba shikkenan wannan gmail din koda kun chanja waya inde gmail din yana nan to dakun dauko app din kun dora gmail din zakuga duk rubutun da kuka ajiye sun dawo

Ga yadda zaku ajiye rubutu acikinsa

bayan kun gama dora gmail din saiku duba zakuga alamar +

Saiku danna anan zakuga wajen da zakuyu rubutu, saiku rubuta duk abun da kukeso, sai kuyi save kuma zaku iya dora hoto ma, duk akwai a wajen

Wannan shine hanyar da zaku ajiye rubutu a ta yadda koda kun chanja wayar zaku dawo da abunku cikin Sauki

Allah ya bada sa’a

Advertisement

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Advertisement
Back to top button
error: Alert: Content selection is disabled!!