Tutorials

Yadda Zaka Sarrafa Wayarka Ta Android Ta Hanyar Amfani Da Hannu Daya

Advertisement Join Our Whatsapp Group

Yadda Zaka Sarrafa Wayarka Ta Android Ta Hanyar Amfani Da Hannu Daya

Assalamu Alaikum Barkanmu Da Wannan Lokaci Sannunmu Da Sake Saduwa Daku A Wannan Shafi Namu Mai Albarka Hikima Tv.

A Cikin Darasin Namu Nayau Zamu Kawo Muku Cikakken Bayani Akan Yadda Zakayi Amfani Da Hannu Daya Wurin Amfani Da Wayarka Ta Android.

Mafi Yawancin Lokuta Ko Muce A Wasu Lokutan Mutum Yana Iya Samun Wata Matsala Irin Ta Rauni Ko Wani Akasi Wanda Sai Kaga Bayason Ko Baya Iya Amfani Da Hannayensa Guda Biyu Wurin Amfani Ko Sarrafa Wayarsa.

To Wannan Dalili Na Daya Daga Cikin Irin Dalilan Da Sukasa Mukayi Kokarin Kawo Muku Wannan Darasi Na Yadda Zakayi Amfani Da Wannan Manhaja Cikin Sauki.

Bari Mu Fara Kawo Muku Cikakken Bayani Akan Wannan Application Bayan Kunyi Download Nasa.

Sannan Zamu Ajiye Muku Link Na Videonsa Wanda Zaku Iya Kalla Daga Baya Idan Baku Fahimci Bayanin Namu Yadda Yakamata Ba.

To Da Farko Bayan Ka Danna Wurin Da Mukace Ku Danna Kayi Ko Kinyi Download Na Wannan Application Saikayi Installing Dinsa, Idan Kuma Wanda Muka Ajiye Muku Baiyiba To Zaku Iya Rubuta Sunan App Din A Google Playstore Kuyi Download Dinsa.

Bayan Kayi Install Saikayi Open Daga Nan Zai Nemi Ka Danna Accept, Bayan Ka Danna Accept Zakaga Wata Alamar Kibiya A Gaba Daga Kasa Saikayi Ta Dannawa Idan Yakawo Ka Wurin Da Zaka Bashi Permission Wato Zaka Danna Wurin Da Aka Rubuta Enable Accessibility, Kana Dannawa Zai Nunama Wurin Da Zaka Danna Kabawa Application Din Damar Hawa Kan Wayarka.

Kana Dannawa Saikayi Open Kanayin Open Zai Tambayeka Ka Danna Allow Kana Dannawa Zai Kawoka Cikin App Din Zakaga Wata Alama A Bude Daga Tsakiyar Appliction Din An rubuta Stop App.

To Wannan Yana Nufin Application Din Yana Aiki Idan Kuma Ka Danna Stop To Zai Daina Aiki, Daga Nan Saika Jawo Gefen Dama Ko Hagu Na Wayarka Da Hannu Daya, Take Zakaga Wata Alama Ta Bayyana Mai Kamar Sanda.

To Daga Sama Zakaga Bata Da Fadi Da Yawa Amma Daga Kasa Tana Da Fadi Sosai To Wannan Abu Zakana Sarrafashi Ne Kamar Mouse Na Computer Wato Kana Tura Alamar Nan Ta Sama Kan Abinda Kakeson Dannawa Saika Danna Tsakiyar Na Kasan.

Ga Link Din Application Din Saiku Danna Download Domin Saukar Dashi Akan Wayoyinku.

Download Quick Cursor Now

Advertisement

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Advertisement
Back to top button
error: Alert: Content selection is disabled!!