Yadda Zaka Dora Iphone Launcher ( Apple ) Akan Wayarka Ta Android
Yadda Zaka Dora Iphone Launcher ( Apple ) Akan Wayarka Ta Android
Assalamu Alaikum Barkanmu Da Wannan Lokaci Sannunmu Da Sake Saduwa Daku A Wannan Shafi Namu Mai Albarka Hikimatv.
A Post Ko Darasin Namu Nayau Zamu Kawo Muku Bayani Ne Akan Wata Sabuwar Launcher Mai Suna Iphone Launcher.
Amma Kafin Mukai Ga Kawo Muku Cikakken Bayani Akan Wannan Application Ko Muce Manhaja, muna Fatan Zaku Kasance Da Wannan Shafi Namu Mai Suna Hikimatv A Kowane Lokaci.
Hakan Bazai Kuma Yiwuba Har Sai Kun Danna Alamar Nan Ta Allow Wanda Take Bayyana Muku A Duk Lokacin Da Kuka Shigo Wannan Shafi Namu.
Danna Wannan Alama Shine Kadai Zaisa Ana Sanar Dakai A Duk Lokacin Da Muka Saki Wani Sabon Darasi Da Dumi-duminsa Mungode.
To A Yau Mun Kawo Muku Bayani Ne Akan Wata Sabuwar Launcher, Munriga Munsan Mafi Akasarin Mutane Ko Da Dama Daga Cikinku Sun San Minene Launcher.
Amma Domin Karin Bayani Yanzu Zamu Kawo Muku Dan Takaitaccen Bayani Akan Minene Launcher.
Da Farko Dai Ita Launcher Kamar Wata Shimfida Ce Dake Cikin Wayar Android, Kai Harma Da Computer Da Sauran Abubuwan Da Bature Ya Kirkira Dominta.
Ita Wannan Manhaja Mai Suna Launcher Ana Amfani Da Itane Idan Anaso A Karawa Waya Kyawun Gani Da Tsari Ammafa Daga Cikin Wayar Ba Daga Wajentaba.
Domin Daga Wajenta Tana Nan A Yadda Ka Sayeta, Indai Ba Fenti Zakaje Ayi Mataba Kaga Ai Babu Abinda Zaisa Ta Sanja Kala.
Amma Ita Wannnn Manhaja Mai Suna Launcher Da Muke Magana Akai Tana Iya Sanja Tsarin Cikin Waya Gaba Daya Kaga Waya Tayi Kyau Ta Sanja Tsari.
Game Son Gwada Wannan Launcher Zaku Iya Danna Wurin Da Aka Rubuta Download Now A Karshen Wannan Posting Namu Domin Kwadawa Wannan Launcher Wata Kila Ta Burgeka.
Idan Kuma Bata Burgeka Ba Zaka Iya Sanja Ta Ta Hanyar Caccaka Home Din Wayarka Kamar Sau Uku Wato Tsakiyar Wayar Domin Launcher Dinka Ta Baya Ya Dawo.
Idan Kuma Ta Birgeka Zaka Iya Cigaba Da Amfani Da Ita, Harzuwa Lokacin Da Zaka Samu Wata.
Ga Link Din Wannan Launcher Saiku Gwada Sauketa Akan Wayoyinku Wata Kila Ta Burgeku Wata Kila Kuma Ta Batawa Wasu Rai Dama Haka Rayuwa Take Abinda Yayiwa Wani, Bashi Ke Yiwa Wani Ba.