Tutorials

Yadda Ake Amfani Da Palm Store Akan Wayar Android 2022

Advertisement Join Our Whatsapp Group

Yadda Ake Amfani Da Palm Store Akan Wayar Android 2022

Jama,a Assalamu Alaikum Barkanmu Da Wannan Lokaci Sannunmu Da Sake Saduwa Daku A Wannan Shafi Namu Mai Albarka Hikimatv.

A Darasin Namu Nayau Zamu Kawo Muku Cikakken Bayani Akan Amfanin Palm Store Dake Kan Wayoyinmu Na Android.

Musamman Ma Wayar Tecno Da Infinix wadda Kusan Dukkan Abinda Yake Kan Waccan To Akwaishi Akan Waccan Wayarma.

Mutane Da Dama Suna Ganin Applications Da Dama A Cikin Wayoyinsu Amma Basu Taba Sanin Ko Tambayar Cewar Shin Ni Minene Amfanin Wancan Application Din Ko Kuma Shin Ni Mi Akeyi Da Wannan Application Din.

To Kamar Yadda Kuka Sani Dai Masu Iya Karin Magana Suna Cewa Rashin Sani Jahilci, Duk Abinda Baka Sanhi Ba To Ka Jahilci Wannan Abun.

Kuma Babu Uzuri Ga Wanda Baisan Abuba Amma Yaki Tambaya Domin An Baka Damar Ka Tashi Ka Nemi Ilimi.

Wannan Dalili Yasa Mukace Bari Yau Mu Kawo Muku Bayani Akan Wannan Application Domin Mun Fahimci Ba Kowane Hankalinsa Yakai Kan Wannan Application Ba.

Kasancewar Shi Wannan Application Yana Da Matukar Amfani Akan Wayoyinmu Na Andorid Amma Mutane Da Yawa Basu San Da Hakaba.

To Da Farko Dai Shi Wannan Application Mai Suna Palm Store Yana Nan Akan Wayoyinmu Na Android Musamman Ma Tecno Da Infinix Idan Wayarka Iphone Ko Samsung Ko Vivo Ko Geneo Ce Bai Zama Lalle Ka Ganshi Ba.

Amma Zaka Iya Download Dinsa Ta Google Playstore, Amma Dai Idan So Samune Ace Ganinsa Kayi Akan Wayarka.

To Wannan Appplication Dai Kamar Yadda Kuke Gani Ko Muke Muku Bayani Wani Store Ne Kamar Playstore Sai Dai Yafi Playstore Applications Din Da Mutane Suke Bukata.

Dalili Na Anan Shine, A Cikin Wannan Store Din Zaka Iya Samun Abubuwa Irin Su Gb Whatsapp Wanda Playtore Bai Yarda Da Irin Wadannan Applications Ba.

Kai A Takaice Zaka Iya Samun Dubban Applications Wanda Babusu A Playstore Kuma Ka Saukar Dasu Akan Wayarka Cikin Sauki.

To Kunga Kuwa Lalle Wannan Application Zai Taimakawa Wadanda Suke Samun Matsaloli Dangane Da Wasu Applications Wadanda Basa Samunsu A Manhajar Playstore.

Mungode Mungode Mungode Sai Mun Hadu Daku A Darasi Na Gaba Inda Muke Fatan Zaku Kasance Da Wannan Shafi Namu Mai Albarka A Kowane Lokaci.

Advertisement

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Advertisement
Back to top button
error: Alert: Content selection is disabled!!