Tutorials

Yadda Ake Boye Dukkan Wani Application, Video, Audio, Files, Pictures Private Browsing A Cikin Wayarka Ta Android

Advertisement Join Our Whatsapp Group

Yadda Boye Dukkan Wani Application, Video, Audio, Files, Pictures Private Browsing A Cikin Wayarka Ta Android

Assalamu Alaikum Barkanmu Da Wannan Lokaci Sannunmu Da Sake Saduwa Daku A Wannan Shafi Namu Mai Suna Hikimatv.

A Darasin Namu Nayau Zamu Kawo Muku Wani Application Ko Muce Manhaja Wadda Zaka Boye Komai Da Komai Cikin Wayarka Ta Android.

Mutane Da Dama Suna Bukatar Sirri, Irin Wannan Sirri Yahada Da Boye Video,Audio, pictures, applications da files akan wayoyinsu na android.

Wannan dalilin ne yasa muka kawo muku wannan darasi wanda munsan zakuyi matukar farin ciki da shi.

Domin zaibaku damar boye dukkan wani abu da bakwason wasu mutane su gani dake kan wayoyinku na android.

Akwai applications masu yawa wadanda ake iya boye abubuwa dasu amma wannan na daya daga cikin wadanda suke da tabbas kuma mungwada mungani.

A karshen wannan bayani namu zamu ajiye muku link din wannan application domin kusamu damar saukar dashi akan wayoyinku cikin sauki.

Amma Kafin mukai ga ajiye muku link din wannan application muna fatan zaku danna alamar allow na notification domin a rika sanar daku a duk lokacin da muka saki wani sabon darasi mungode.

To Da farko bayan kasaukar da wannan manhaja wato application saikayi installing dinsa, bayan kayi installing dinsa saikayi open.

Kanayin open zai baka damar zabar pattern din da kake son sanyawa wanda zai zamemaka security na kan wannan application.

Bayan kasaka ka kara maimaitawa zai kaika cikinsa to anan zakaga wurinda aka jera maka dukkan applications din dake kan wayarka ko ince wadanda kayi installing dinsu.

Daga gaban sunan ko wanne application zakaga alamar lock wato rufewa to saika zabi applications din da kakeson rufewa ka danna wannan alama ta lock.

Kana dannawa Zasu umarceka dacewar kanemi wannan application daga cikin jerin application din da suka watsoma saika taba sunan ” app lock ” din saika bashi dama.

Kana dannawa shikenan wannan abunda ka rufe ya rufu, haka zakayi ta danna lock na dukkan application din da kakeson rufewa.

Sannan daga sama idan kanason rufe waka ko video ko hoto ko file to akwai wani wuri da aka rubuta ” vault ” Saika danna wannan wurin.

Kana dannawa zakaga polder din video audio file apk, to anan saika danna kan sunan abinda kakeson boyewa.

kana dannawa zakaga wata alama ta + saika dannata kana dannawa zai watsoma dukkan videos ko audios din dake kan wayarka saikayi select na abinda kakeson boyewa.

Haka zakabi wannan hanya idan zaka boye dukkan wani abu da kake bukata idan kuma kana bukatar ka budesu to zaka iya zuwa ka danna kansu kayi unhide.

Ga application dinnan saiku saukar dashi izuwa kan wayoyinku idan kuma baka fahimci yadda zakayi ba to ga link din video nan a kasa saika kalla domin ganewa idanuwanka.

Ga Link Din Application Din.

Download Now

Ga Link Din Videon.

Kalli Videon Anan

Advertisement

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Advertisement
Back to top button
error: Alert: Content selection is disabled!!