Tutorials

Yadda Zaka Saurari Wakoki Guda Biyu Da Earpiece Guda Daya A Wayarka Ta Android 2022

Advertisement Join Our Whatsapp Group

Jama,a Assalamu Alaikum Barkanmu Da Wannan Lokaci Sannunmu Da Sake Saduwa Daku A Cikin Wannan Shafi Namu Mai Albarka Hikimatv.

A Darasin Namu Nayau Zamu Kawo Muku Cikakken Bayani Akan Wani Application Wanda Zaka Samu Damar Sauraren Wakoki Guda Biyu Ta Hanyar Amfani Da Earpiece Guda Daya.

Munsan Wannan Abu Zaiyi Matukar Baku Mamaki Amma Idan Akace Zamani To Babu Mamaki Domin Shi Zamani Yafi Karfin Komai.

Abinda Muke Fata Shine Ku Karanta Wannan Bayani Tun Daga Farko Har Karshe Domin Fahimtar Yadda Zakuyi Amfani Da Wannan Manhaja Cikin Sauki.

Sanin Kanku Ne Akwai Players Na Sauraron Wakoki Da Dama Amma Nasan Baku Taba Cin Karo Da Player Wadda Take Da Irin Wannan Abun Mamakin Ba.

Wannan Dalili Yasa Mukace Bari Mu Kawo Muku Bayani Akan Wannan Player Wanda Kuma A Take Zaku Iya Gwadawa.

A Karshen Wannan Bayani Namu Zamu Ajiye Muku Link Na Wannan Player Domin Ku Samu Damar Saukar Da Ita Cikin Sauki.

Sannan Idan Wannan Bata Muku Aiki Ba Zaka Iya Duba Sunanta Sai Kayi Searching A Playstore Domin Ka Saukar Wadda Zata Yiwa Wayarka.

To Bayan Kayi Download Na Wannan Player Saikayi Installing Dinta Kayi Open Bayan Kayi Open Zakaga Ta Rabama Wayarka Gida Biyu A Kwance.

To A Sama Zakaga Wurin Da Aka Rubuta ” Load To Play Left Track ” To Wannan Suna Bayanin Cewa Ka Danna Wannan Wuri Domin Kunna Wakar Da Kake Son Ji A Kunnenka Na Hannun Hagu.

Kana Danna Wannan Wuri Zai Kaika Shafi Na Gaba Inda Zaka Danna Wurin Da Aka Rubuta ” Library ” Zakaga Wannan Wuri Daga Sama Chan A Hannun Dama, Kana Ganin Wannan Wuri Saika Danna Take Zai Kaika Wani Shafin Wanda Zaka Danna ” All Music ” Kana Bukatar Ganin Dukkan Wakokin Dake Kan Wayarka.

Kana Dannawa Zakaga An Watsoma Duk Wakokin Kan Wayarka, Domin Kadda Ka Wahalar Da Kanka Zaka Iya Taba Wurin Da Aka Alamar Searching Daga Sama Saika Rubuta Sunan Wakar Da Kake Son Kunnawa Kayi Search Kanayi Zakaga Wakar Saika Danna Kanta.

Kana Dannawa Take Wakar Zata Fara Play, Kana Ganin Haka Saika Dawo Baya Wato Ka Danna Back Ka Taba Daya Wurin Dayake Kasa Domin Zabar Wakar Da Kakeson Ji A Kunnenka Na Dama.

Yadda Kayi Wajen Kunna Na Kunnen Hagu Haka Zakabi Wannan Hanya Domin Kunna Ta Kunnen Dama.

Idan Kana Da Tambaya Zaka Iyayi Ta Hanyar Yin Comment, Sannan A Cikin Wannan App Zaka Iya Searching Na Wakoki Sabi.

Mungode Mungode Ga Link Din Wannan Application Saiku Danna Wurin Da Aka Rubuta Download Now Domin Saukeshi Zuwa Kan Wayoyinku.

Download Now

Advertisement

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Advertisement
Back to top button
error: Alert: Content selection is disabled!!