Yadda Zaku Dawo Da Numbers Din Wayoyinku Koda An Sacema Wayarka Ko Karasa Layinka.
Jama,a Assalamu Alaikum Barkanmu Da Warhaka Sannanunmu Da Sake Saduwa Dakuma Jamewa Daku A Cikin Wani Sabon Posting Mai Suna ” Yadda Zaka Dawo Da Numbobin Kan Wayarka Koda An Sace Ko Karasa Layin Wayar Taka”.
To A Cikin Wannan Post Dazamu Kawo Muku Muna Bukatar Da Ka Karanta Wannan Bayani Gaba Daya Domin Hakan Shi Zai Taimakama Wurin Fahimatar Yadda Zakayi Wannan Aiki Batare Da Ka Samu Wata Matsala Ba.
To Da Farko Dai Abinda Zakayi Shine, Mallakar Gmail Account, Wasu Kuma Suna Kiransa Da Email, To Koma Dai Minene Duk Dayane Da Gmail Da Email Duk Abu Dayane Amma Dai A Yanzu Sunan Da Akafi Kiransa Dashi Shine Gmail.
To Bayan Ka Tabbatar Dacewar Kana Da Gmail Account, Saika Dorashi Akan Wayanka, Idan Kuma Yana Kan Wayan Naka To Babu Bukatar Ka Kara Dorashi.
Bayan Ka Tabbatar Da Cewar Yana Kan Wayanka Saika Hau Kan Appliction Din Wayanka Mai Suna ” Phone “.
Bayan Ka Hau Kan Phone, Wato Inda Kake Kirafa Kenan Saika Danna Numbers Wato Kayi Kamar Zakayi Save Na Wata Number To Bayan Ka Saka Number Din Saika Shiga Wurin Save To Anan Zakaga Wurin Da Yake Nunama Cewar Akan Sim Ko Phone Ko Gmail Zakayi Save Na Wannan number To Anan Saika Zabi Gmail Kayi Save.
Abinda Ake Bukata Anan Shine Duk Lokacin Da Zakayi Save Na Number Din Da Aka Baka To Kayi Save Dinta Akan Gmail Matukar Kanayin Haka To Bazaka Taba Rasa Numbers Naka Ba Koda Kuwa Layin Wayanka Ya Bata Ko Ansacema Wayanka.
Sannan Wani Abu Na Birgewa Dangane Da Wannan Tsari Na Dora Gmail Ko Muce Saving Na Phone Contact Akan Gmail Shine.
Idan Akan Sim Card Din Wayarka Ko Kan Phone Din Wayarka Zakayi Save Na Contact To Bazakayi Save Na Numbobi Sama Da Dari Biyu Da Wani Abunba.
Amma Idan Akan Gmail Zakayi Save To Zaka Iya Save Na Contacts Sama Da Dubu Goma, Kai A Takaicema Dai Babu Iyaka Domin Shi Kan Gmail Dinka Ba Kamar Kan Waya Ko Sim Card Dinka Bane, Zaka Iya Save Na Contacts Unlimited.
Sannan A Wani Bangare Na Daban Nasan Wannan Matsala Tana Cimuku Tuwo A Kwarya Wace Matsala Ce ?.
Amsa Idan Zaka Saver Number Akan Wayanka Bayan Kasa Number Din Idan Kazo Rubuta Suna Idan Sunan Yana Da Tsayi To Baka Samun Damar Rubuta Shi Sai Dai Kayi A Takaice, To Idan Akan Gmail Zaka Saver Numbobinka To Zaka Iya Saver Ko Wane Irin Sunane Komai Tsayinsa.
ToKaga Kuwa Wannan Wata Damace Wanda Basaikana Ta Siyan Layikan Waya Kana Saver Contacts Dinka Ba, Ta Hanyar Amfani Da Gmail Kawai Zaka Samu Damar Kawar Da Waccan Matsalar Batare Da Kashiga Wani Rudani Ba.
Idan Kana Da Ko Kina Da Tambaya Zaka Ko Zaki Iya Ajiye Comment Domin Karin Bayani Sannan Anan Gaba Ko Muce A Wani Sabon Posting Din Zamu Kawo Muku Bayani Akan Yadda Zaku Duba Duk Wani Video Ko Bayani Akan Abubuwan Da Muke Kawo Muku Ta Hanyar Amfani Da Manhajar Youtube.
Saiku Kasance Da Wannan Site Namu Mai Suna hikimatv.ginsau.com.ng Domin Samun Sababbin Shirye-shiryenmu Akowane Lokaci Kuma Da Zarar Munsakeshi Ta Hanyar Danna Alamar Allow Dake Kan Wannan Site Namu Mungode Mungode Mungode Sai Mun Hadu A Posting Na Gaba.