Tutorials

Shin Pi-Network Zai Zo Akan $314000 ? Ga Maganar Gaskiya Dangane Da Wannan Farashi.

Advertisement Join Our Whatsapp Group

Shin Pi-Network Zai Zo Akan $314000 ? Ga Maganar Gaskiya Dangane Da Wannan Farashi.

Assalamu Alaikum Barkanmu Da Wannan Lokaci Sannunmu Da Sake Saduwa Daku A Wannan Shafi Namu Mai Albarka Hikimatv.

A Cikin Darasin Namu Nayau Zamu Kawo Muku Cikakken Bayani Akan Irin Farashin Da Pi- Network Zai Iya Zuwa Dakuma Bayani Akan Masu Cewa Pi Zai Zo Akan Dala Dubu Dari Uku Da Goma Sha Hudu.

Da Farko Dai Kamar Yadda Bincike Ya Nuna Mafi Yawancin Mutanen Da Suke Cewa Pi Network Zai Zo Akan Wannan Kudin To Basu Sanma Minene Harkar Coins Ba.

Domin Koshi Kansa Bitkoins Baizo Akan Wannan Farashin Da Suke Tunanin Pi Zai Zo Akansaba.

Sannan Abinda Bincike Ya Nuna Babu Wata Jarida Ko Majiya Mai Karfi Da Suka Duba Wadda Ta Tabbatar Musu Dacewar Pi Zaizo Akan Wannan Kudi, Kawai Dai Suna Yanki Fadi Ne.

Wannan Yanki Fadi Da Sukeyi Shine Yasa Mutanen Da Sukuma Basu Da Ilimin Komai Sukema Karyata Pi Din Gaba Dayansa.

To Maganar Wannan Kudi Ba Gaskiya Bane A Yanzu Amma Wata Kila Nan Da 10 To 20 Years Ya Iya Kaiwa Wannan Kudi Da Ake Fada, Shima Kuma Babu Tabbas.

Abin Lura Shine Yakamata Mutane Suna Tunani Akan Yadda Ake Samun Kudi, Su Kansu Turawan Nan Fa Sai Sunsha Wahala Suke Samun Kudi.

Sannan Ba,a Shekara Daya Ko Biyu Ko Uku Sukayi Wannan Kudin Ba, Sannan Abinda Zaka Duba Idan Akace Za,a Sayi Pi Akan Wannan Kudi To Wanene Zai Baka Wannan Kudin ? Sannan Idan Ya Saya Wanene Zai Bashi Riba Akan Kudin Daya Kashe.

Ga Dan Kankanin Misali Wallahi Bature Da Kake Gani Yafika Son Kudi Yafika Iya Neman Kudi, Domin Kuwa Yana Iya Sadaukar Da Rayuwarsa Domin Ya Nemi Kudi Yayin Da Kaikuma Kake Kwance Ka Kasa Fita Kasuwa.

To Maganar Gaskiya Wannan Pi Da Kuke Gani Zai Iya Zama Wani Abu Amma Ba Yanzu Ba Ba Kuma Nan Da 1 To 2 Years Ba.

Kawai Dai Ka Adana Bayanan Ka Domin Wata Kila Idan Ka Haura Shekara 30 Sai Dai Yayanka Su Gada Amma Kai Babu Rabonka, Domin Ta Iyu A Lokacin Ka Daina Jindadin Abinci.

Mutane A Rage Buri, Wadanda Ke Karyata Pi A Daina Ana Karyata Kudinsa Domin Dama Bazai Taba Zuwa Akan Wannan Kudinba, Amma Zai Iya Zama Gaskiya.

Domin Koda Da Wasa Suka Kirkireshi To Ganin Yadda Suka Tara Mabiya To Zasu Iya Maidashi Da Gaske, Abin Lura Aka Aka Fara Akan Bitkoins Shima Abune Kamar Wasa Amma Yazama Gaskiya.

Adaina Karyata Abinda Baka Sanshi Ba, Sannan Adaina Kashewa Mutane Kwarin Gauwa Akan Wani Abu Da Sukeyi Matukar Ba Sabon Allah Bane.

Don Haka Idan Kai Bazakayi Ba, To Kaja Bakinka Kayi Shiru Tunda Baka Da Interest, Kai Kuma Wanda Kake Mining Yakamata Kadaina Damun Wadanda Basu Da Interest Duk Mutumin Da Kasan Zaiyi Saika Fadamasa, Wanda Kuma Bazaiyiba Saika Rabu Dashi.

Allah Yabamu Sa,a Yasa Mucika Da Imani Anan Gidan Duniya Da Lahira, Sannan Sai Anayi Ana Hakuri Da Juna.

Advertisement

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Advertisement
Back to top button
error: Alert: Content selection is disabled!!