Tutorials

Yadda Zaka Saukar Da Advance Learners Dictionary Akan Wayarka Ta Android

Advertisement Join Our Whatsapp Group

Yadda Zaka Saukar Da Advance Learners Dictionary Akan Wayarka Ta Android.

Assalamu Alaikum Barkanmu Da Wannan Lokaci Sannunmu Da Sake Jamewa Daku A Wannan Shafi Namu Mai Albarka Hikimatv.

A Cikin Darasin Ko Posting Din Da Zamu Kawo Muku A Yau Zamu Kawo Muku Wani Babban Application Mai Matukar Amfani.

Wannan Application Zaiyi Matukar Taimaka Muku Musamman Ma Dalibai Wadanda Basu Da Dictionary Wanda Zasuna Duba Kalmomin Da Basu Sani Ba.

To Matukar Ka Mallaki Wannan Application To Zakayi Matukar Farin Ciki Wurin Duba Kalmomin Da Baka Sani Ba.

Wannan Dictionary Yana Dauke Da Abubuwa Irinsu ” Google Translator” 500 Difficult Words ” Tare Da Conversation Wato Yadda Ake Magana.

Minene Google Translator ?.
Amsa: google translator wani application ne wanda zaka iya amfani dashi wurin juya fassarar wani yare zuwa wani yare.

Matukar ka mallaki wannan dictionary to zaka samu wannan translator a cikinsa wadda hakan zaiyi matukar taimaka maka wurin koyan turanci.

Domin zaka iya rubuta wani abu da hausa kuma ka maidashi izuwa turanci, sannan zaka iya rubuta wani abu da turanci ka maidashi izuwa hausa.

Duba da matsalolin da ake ta samu a bangaren koyon turanci yasa mukayi kokari muka lalubo muku wannan application domin munsan zaiyi matukar taimakawa dalibai.

Haka zalika ba dalibai kadai wannan application zai taimakawa ba, nasan dai duk iliminka har yanzu oxford yafika ilimi dole akwai kalmomin da baka sansu ba kuma baka taba ganinsu ba.

To kaga kuwa wannan application zai iya yima amfani koba yanzu ba,amma fa mai tunani ne kadai zai iya gane hakan.

A karshe zamu ajiye muku link na wannan application mai suna advance learners dictionary domin kusamu damar saukar dashi cikin sauki.

Ga Link Din Application Dinnan Saiku Danna Wurin Da Aka Rubuta Download Now Domin Saukar Da Wannan Manhaja.

Download Now

Advertisement

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Advertisement
Back to top button
error: Alert: Content selection is disabled!!