Yadda Zaka Karawa Wayarka Sauri Ta Hanyar Goge Duk Wani Abinda Yake Kamarda Ita.
Yadda Zaka Karawa Wayarka Sauri Ta Hanyar Goge Duk Wani Abinda Yake Kamarda Ita.
Jama’a Assalamu Alaikum Warahamatullahi Wabarakatuhu, Barkanmu Da Wannan Lokaci Sannunmu Da Sake Jamewa Daku A Wannan Shafi Namu Mai Tarin Albarka Hikimatv.
In Ayau Zamu Kawo Muku Bayani Cikakke Akan Wani Application Ko Muce Manhaja Wadda Zata Taimaka Muku Sosai A Wasu Bangaren Karawa Wayoyinku Sauri A Lokacin Da Kuke Amfani Da Ita.
Kamar Yadda Mukasha Kawo Muku Abubuwa Da Dama Dasuka Danganci Wayoyin Hannu Na Android To Ayauma Munkawo Muku Wani Application Wanda Zai Tamaka Muku Wurin Saurin Download Ko Wasu Bangaren Na Wayoyinku.
Dalilin Dayasa Muka Kawo Muku Wannan Darasi Shine Wasu Da Dama Musamman Wadanda Wayoyinsu Basu Da Ram Mai Yawa Suna Korafi Akan Cewar Wayoyinsu Suna Yawan Kame Musu.
To Wannan Shine Dalilin Dayasa Muka Kawo Muku Wannan Darasi Domin Kawar Muku Da Wannan Matsala.
Muddin Ka Mallaki Wannan Application To Zaka Samu Sauki Kamewar Da Wayarka Takema A Duk Lokacin Da Kake Amfani Da Ita.
A Gaba Kadan Zamu Ajiye Muku Link Din Wannan Application Domin Saukaka Muku Wurin Download Na Wannan Application.
Da Farko Dai Bayan Kayi Download Na Wannan Application Kayi Installing Dinsa Saikayi Open Dinsa.
Bayan Kayi Open Zai Nemi Kabashi Dama, Sai Ka Danna Allow Zai Kaika Wani Shafin Da Yakeso Ka Danna Wurin Da Aka Rubuta Sunansa Ka Bude Wata Alama.
Kana Budewa Saika Danna Back, Daga Nan Zai Kara Neman Kabashi Dama Bayan Ka Bashi Duk Wata Dama Zai Kawoka Cikinsa.
To Anan Zakaga Wurin Da Aka Rubuta Sd Card Wato Memory Kana Danna Wannan Wuri Zai Kaika Cikinsa To Saika Danna Wurin Scan To Anan Zata Gogema Duk Wani Abu Dayake Tsayar Da Wayarka.
Zaka Iya General Scan Domin Ta Gogema Duk Wani Abu Dayake Tsayarma Da Wayarka.
Ga Link Din Application Dinnan Saiku Danna Wurin Download Now Domin Saukar Dashi Izuwa Kan Wayoyinku Mungode.