Tutorials

Yadda Zakayi Kira Na Tsawon Mintuna 20 Akan Kudi Naira #100 Kachal A Kowane Layin MTN

Advertisement Join Our Whatsapp Group

Yadda Zakayi Kira Na Tsawon Mintuna 20 Akan Kudi Naira #100 Kachal A Kowane Layin MTN

Assalamu Alaikum Barkanmu Da Wannan Lokaci Sannunmu Da Sake Saduwa Daku A Cikin Wannan Shafi Namu Mai Albarka Hikimatv.

A Darasin Namu Nayau Zamu Kawo Muku Cikakken Bayani Akan Yadda Zaku Samu Damar Yin Kira Na Tsawon Mintuna 20 Kaga Wannan Garabasa Ce Mai Girma Ga Dai Bayanin Nan Saiku Karanta A Nutse Domin Kusan Yadda Ake Shiga Wannan Tsari.

Abinda Yasa Nayi Wannan Posting Shine :

Ganin mutane da dama suna son su sami sauƙi yayin kiran waya, shi ne yasa ma har su ke siyan Layin Airtel RCCG domin samun yin waya mai tsawo akan kuɗi ƙalilan.

Ganin kwanakin nan Airtel sun Dakatar da mutane da yawa wannan tsarin, kuma mutane suna son samun sauƙin kira, domin cajin da ake musu ya yi yawa, shi yasa na ce bari in sanar da ku wannan hanyar, ko zaku sami sauƙi a kan yadda ake cajin ku.

Abubuwan da ake buƙata:

Layin MTN ( Mtn sim card )
Tsarin Beta Talk ( Tsarin Mtn ne )
Katin waya (Recharge card )

Yadda Ake shiga Tsarin beta talk Ka danna *123* *1*1#.

Tsarin Beta Talk suna ba da bonus ₦300 akan duk katin ₦100 da ka saka.

Bayan ka shiga Beta Talk sai ka saka katin waya na ₦100.

YADDA ZAKA JUYA KATINKA YA KOMAI MINTUNA 12.

Ka danna *567*119*1*1# sai ka kira.

Idan bai yi ba, sai ka je wajen message ka rubuta 100 sai ka tura zuwa 567.

Za su ba ka Zaɓi (option) sai ka Zaɓi 1 ko 2.

Za su ba ka ₦120 da kuma 100Mb.

Duk sanda ka saka kati kawai haka za ka yi.

Kana da bonus 300 yanzu kuma ka sami 120, Insha Allah za kai mintuna 20 ko fiye da haka.

Note: ka tabbatar da ƙaramar waya ka ke aiki da Layin, domin idan da babbar waya ka ke yi, da zarar datarka ta ƙare, bonus ɗinka na 300 za a fara ɗiba wajen yin browsen.

Duk Mai tambaya akan Mtn zai iya tambaya ta ta inbox, idan na sani zan ba shi amsa.

Mungode Mungode Sai Mun Hadu Daku A Wani Darasin Anan Gaba Inda Muke Fatan Zaku Kasance Da Wannan Shafi Namu Mai Albarka Mungode.

Advertisement

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Advertisement
Back to top button
error: Alert: Content selection is disabled!!