Tutorials

Yadda Zaka Hana Youtube, Google, Ko Mutane Bibiyarka Ko Ganin Abubuwan Da Kakeyi A Cikin Wayarka.

Advertisement Join Our Whatsapp Group

Yadda Zaka Hana Youtube, Google Ko Gmail Bibiyarka Ko Ganin Abubuwan Da Kakeyi A Cikin Wayarka.

Jama,a Assalamu Alaikum Barkanmu Da Wannan Lokaci Sannunmu Da Sake Saduwa Daku A Cikin Wannan Shafi Namu Mai Suna Hikimatv.

A Darasin Namu Nayau Zamu Kawo Muku Cikakken Bayani Akan Yadda Zaka Hana Google Bibiyar Irin Ayyukan Da Kakeyi.

Abinda Muke Fata Shine Ka Tsaya Ka Karanta Wannan Bayani Step By Step Domin Fahimtar Yadda Abin Yake Domin Tsallake Wani Wuri Zai Iya Sa Kayi Abin Ba Dai Dai Ba.

Da Farko Abinda Zakayi Batare Da Bata Wani Lokaci Ba Shine Shiga Setting Wato Kan Setting Na Wayarka Bayan Da Ka Tabbatar Dacewar Ka Dora Gmail Account Dinka Akan Wayarka.

To Da Farko Dai Zaka Shiga Setting Din Kan Wayarka Daga Nan Saika Ja Zuwa Kasa Ka Duba Wurin Da Aka Rubuta ” Google “.

Bayan Ka Danna Kan Google Zai Kaika Zuwa Shafi Na Gaba Inda Zaka Danna Wurin Da Aka Rubuta ” Manage Your Google Account ” Kana Danna Wannan Wuri Zai Danyi Searching Inda Zai Kaika Shafi Na Gaba Wanda Zakaga Wasu Da Akayi Wasu Rubutu Kamar Haka.

Na Farko Zakaga ” Home ” Na Biyu Zakaga ” Personal Info ” Na Uku Zakaga ” Data & Privacy ” Na Hudu Zakaga Wurin Da Aka Rubuta ” Security ” Wato Idan Kadan Jawo Rubutun Zuwa Hannunka Na Hagu.

To Idan Kazo Wannan Wuri Zaka Danna Wurin Ko Kan ” Data & Privacy ” Bayan Ka Danna Wannan Wuri Zai Kawoka Wani Shafi Inda Zaka Dan Ja Zuwa Kasa.

Idan Kaja Zuwa Kasa Zakaga Wasu Wurare Guda Uku Wadanda Aka Rubuta ” Web & App Activity ” Na Biyu Kuma Zakaga An Rubuta ” Location History ” Na Uku Kuma Zakaga An Rubuta ” Youtube History.

To Bari Mu Kawo Muku Cikakken Bayani Akan Kowane Daya Daga Cikinsu.

Na Farko Dai Shine ” Web & App Activity ” Wanda A Hausance Suna Nufin Duk Wani Browsing Ko Applications Da Kake Amfani Dasu To Google Suna Ajiye Wannan Bayanai Kuma Suna Ganin Dukkan Abinda Kakeyi.

To Illar Wannan Abu Shine Duk Lokacin Da Wani Ya Karbi Wayarka Zai Iya Sanin Dukkan Password Ko Gmails Ko Wani Browsing Da Kakeyi Ko Wani Website Da Kake Shiga To Rufe Wannan Wuri Zaisa Babu Wani Mahaluki Dazai Iya Bibiyar Browsing Ko Amfani Da Wani Application Da Kakeyi.

Idan Kanaso Ka Rufe Wannan Wuri To Kai Tsaye Zaka Danna Wurin Da Aka Rubuta ” Web & App Activity ” Kana Dannawa Zai Kawoka Zuwa Wani Shafi Wanda Anan Ne Zaka Danja Zuwa Kasa Idan Ka Duba Daga Hannun Dama Zakaga Wurin Da Aka Rubuta ” Turn Off “.

Kana Danna Wannan Wuri Zai Kara Watsoma Shafin Da Zaka Kara Danja Zuwa Kasa Saika Danna ” Pause ” Kana Dannawa Shikenan Ka Rufe Wannan Wuri.

To Daga Wannan Lokaci Babu Mai Kara Bibiyar Irin Abubuwanda Kakeyi A Website Ko Application, Sai Dai Illar Hakan Itace Idan Ka Manta Password Dinka Ko Wasu Details To Bazaka Kara Samunsu Ba Har Sai In Tunawa Kayi.

Akasin Idan Wurin A Bude Yake Zasu Rika Yima Save Na Duk Wasu Bayanai Dakata Taba Ajiyewa Aciki.

Abu Na Biyu Shine ” Location History ” Wanda Shine Babban Abinda Yafi Kamata Ka Rufe Domin Barin Wannan Wuri A Bude Shine Zaisa Duk Wani Wanda Yake Bibiyarka Yasan A Inda Kake Kama Daga Kasa, Haja Da Kuma Local Govenment.

To Wannan Wuri Yana Da Kyau Ka Rufeshi Domin Saboma Dashine Muka Kawo Muku Wannan Bayani.

Abu Na Uku Wanda Shine Na Karshe Shine ” Youtube History ” Shi Wannan Youtube History Yana Bayyana Irin Dukkan Abubuwan Da Kake Aikatawa Ne Akan Youtube Yana Ajiye Bayanai Akai.

Idan Har Bakaso Asan Abubuwan Da Kake Aikatawa Akan Youtube To Saikaje Ka Rufe Wannan Wuri To Daga Wannan Lokaci Koda Kayi Searching Na Wani Abu Idan Ka Fita Ka Dawo Zaka Tarar Babu Alamar Ko Tarishin Cewar Kayi Wannan Bincike.

Mungode Mungode Mungode Inda Dukka Dukka Anan Muka Kawo Karshen Wannan Darasi Inda Muke Fatan Zaku Kasance Da Wannan Shafi Namu Domin Samun Sababbin Shirye-shiryenmu Akowane Lokaci.

Advertisement

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Advertisement
Back to top button
error: Alert: Content selection is disabled!!