Tutorials

Abinda Yakamata Kowane Mai Amfani Da Gmail, Whatsapp, Facebook, Pi Network Da Satoshi Yasani.

Advertisement Join Our Whatsapp Group

Abinda Yakamata Kowane Mai Amfani Da Gmail, Whatsapp, Facebook, Pi Network Da Satoshi Yasani.

Jama,a Assalamu Alaikum Barkanmu Da Wannan Lokaci Sannunmu Da Sake Saduwa Daku A Cikin Wannan Shafi Namu Mai Albarka Hikimatv.

A Darasin Namu Nayau Zamu Kawo Muku Bayani Ne Akan Yadda Barayi Suke Bin Wasu Hanyoyi Wurin Bincike Ko Daukan Wasu Bayanai Akan Wayarka Ta Android.

A Wannan Lokaci Da Muke Ciki Na Neman Tsira, Zakaga Mutane Da Dama Suna Ta Kokarin Cike Wasu Abubuwa Domin Samun Kudi Ko Yin Wasu Al,amura.

To A Dai Dai Wannan Lokaci Ne Barayi Ko Ince Wasu Mutane Suke Amfani Da Wannan Dama Wurin Kirkirar Wata Manhaja Wato ( Application ) A Turance Ko Kuma Link Da Akebi Wurin Cike Wani Abu Suna Satar Bayanan Mutane.

Wadannan Mutane Sun Dade Sosai Suna Wadannan Abubuwa Batare Da Labari Yakai Ga Wadansu Ba.

Wani Lokacin Zakaga Anyiwa Wani Amma Saboda Rashin Jindadin Da Yayi Ko Kuma Saboda Mugunta Bazai Yiwa Wasu Bayani Akan Wannan Matsala Ba, Kasan Hausawa Da Bakar Zuciya.

To Duba Da Irin Wadannan Abubuwa Dake Faruwa A Cikin Al,umma Yasa Mukace Bari Mu Kawo Muku Bayani Akan Wannan Abu Dake Faruwa Domin Ko Kai Baka Samu Kanka A Cikin Irin Wannan Matsala Ba To Sai Kayi Kokari Kayiwa Wadanda Suke Irin Wadannan Abubuwa Da Zamu Lissafo A Kasa.

Misali Zakaga Wasu Mutane Suna Harkar Cike Mpower Ko Nirsal Ko Survival Dadai Sauransu, sannan Akwai Wasu Wadanda Suke Cike Wasu Abubuwanma Da Ake Samun Kufi.

Yadai Danganta Da Nitsewar Da Kayi A Cikin Wannan Harka, to Domin Kare Kanka Daga Fadawa Izuwa Tarkon Irin Wadannan Mutane Wadanda Suke Amfani Da Wani App Ko Link Su Dinga Diban Ko Satar Bayanan Wayarka Saikaci Gaba Da Karanta Wannan Bayani Tun Daga Farko Har Karshe.

Irin Wadannan Mutane Suna Amfani Da Wani Application Wanda Zasuce Kayi Register Zaka Samu Kaza Ko Ka Danna Kan Wannan Link Din Domin Samun Kaza.

To Maganar Gaskiya Ba Kowane Link Ko Application Bane Ake Samun Kudi Idan Kayi Register, Ainishima Wadanda Ba,a Samun Komai Sunfi Yawa.

To Domin Gane Link Din Da Aka Turoma Bashi Da Matsala Zaka Iya Ziyartar Wani Shafi Mai Suna Virus Total Ta Chrome Browser Dinka.

Idan Shafin Ya Bude Saikayi Copy Na Wancan Link Din Da Kake Son Tabbatarwa Idan Babu Matsala A Cikinsa Sai Kadawo Cikin Wannan Site Din Kayi Post Dinsa.

Daga Nan Zakaga Wani Wuri Daga Kasa Da Aka Rubuta Check Or Scan Saika Taba Wannan Wuri Take Zakaga Yana Searching Na Gaba Dayan Wannan Link To Anan Zai Nunama Idan Akwai Matsala A Cikin Wannan Link Idanma Babu.

Sannan Abu Na Biyu Dazakayi Shine Zakaje Ka Rufe Location Na Wayarka Amma Zaka Bude Na Iya Bluetooth Da Wifi Saboda Turi Dazakanayi Ta Zanda.

Domin Yin Wannan Abu Zaka Shiga Setting Na Wayarka, Saika Shiga Wurin Da Aka Rubuta “Location ” Wasu Wayoyin Kuma Zakaga An Rubuta ” Security And Location ” Ko Kuma Dai Da Wani Abun Daban Yadai Danganta Da Irin Wayarka.

To Kana Shiga Wannan Wuri Da Aka Rubuta Location Zaka Danna Wurin Da Aka Rubuta ” Wifi And Bluetooth Scanning ” Kana Shiga Wannan Wuri Saika Bude Su Gaba Daya.

Daga Nan Zaka Danna Back Saika Rufe Location Din Daba Daya, To Koda Wani Yana Bibiyar Wayarka Ko Yana Bibiyar Wasu Abubuwa Da Kakeyi Daga Wannan Lokaci Ya Daina Ganin Abubuwan Da Kake Aikatawa.

Domin Su Irin Wadannan Mutane Suna Iya Satar Bayananka Gaba Daya Irin Su Gmail Dinka, Facebook Dinka, Whatsapp Dinka Dai Dai Sauran Wasu Abubuwa Masu Amfani Dake Cikin Wayarka.

Kuma Abin Lurama A Yanzu Da Wadanna Harkoki Guda Biyu Suke Dab Da Tabbata Wato Harka Pi Da Core, Wato Satoshi, Kaga Kuwa Da Zarar Harkar Ta Tabbata To Zasu Iya Debe Komai Nakan Wayarka Tunda Daman Suna Iya Ganin Duk Wasu Bayanan Ka.

Advertisement

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Advertisement
Back to top button
error: Alert: Content selection is disabled!!