Tutorials

Abubuwan Dake Jawo Facebook Suyi Blocking Din Account

Advertisement Join Our Whatsapp Group

Abubuwan Dake Jawo Facebook Suyi Blocking Din Account Dinka Batare Da Kasan Abinda Ka Aikataba.

Jama,a Assalamu Alaikum Barkanmu Da Wannan Lokaci Sannunmu Da Sake Saduwa Daku A Cikin Wannan Shafi Namu Mai Tarin Albarka.

A Cikin Wannan Shafi Namu Mai Suna Hikimatv, Zamu Kawo Muku Cikakken Bayani Akan Dalilan Ko Abubuwan Da Sukesa Facebook Suyi Block Ko Locking Din Account Dinka.

Amma Kafin Mukai Ga Yimiku Cikakken Bayani Akan Wannan Darasi Muna Rokon Da Ku Dinga Danna Mana Alamar Allow Idan Har Alamarta Ta Fito A Duk Lokacin Da Kuka Shigo Wannan Shafi Namu.

Muna Bukatar Da Farko Ku Karanta Wannan Bayani Tun Daga Farko Har Karshe Domin Fahimtar Yadda Abin Yake, Domin Tsalle Wani Wuri Zai Iya Hanaka Fahimtar Ko Sanin Wadannan Dalilai.

To Abu Na Farko Da Yakamata Kusani Shine Facebook Basa Son Yawan Adding Na Friend A Lokacin Daka Bude Sabon Account.

Wannan Yasa Duk Wanda Yabude Account Sabo Suke Bashi Damar Adding Na Mutum Biyar Da Farko, Daga Baya Kuma Suce Kayi Add Na Mutum Goma Sha Biyar.

To Tun Daga Wannan Lokaci Basa Kara Tambayar Mutum Ko Su Bashi Shawara Ko Umarnin Yayi Adding Din Wani Mutum.

Abinda Ake Bukata Anan Shine, Zaka Iya Adding Amma Kadda Yawuce Mutum Goma A Kullum, Idan Abin Ya Ware Wato Facebook Dinka Yayi Kamar Wata Daya Kana Charting Kana Dan Posting Jifa Jifa, To A Wannan Lokaci Zaka Iya Adding Na Mutum Dari Kullum.

A Haka A Haka Har Kaje Adadin Mutum Dubu Biyar Wadda Daga Haka Bazaka Kara Adding Na Kowaba Domin Adadin Friends Din Da Zaka Iya Addin Sune Dubu Biyar Kawai.

Abu Na Biyu Shine, Zakaga Wasu Sun Bude Facebook Kuma Bai Dau Wani Lokaci Kamar Shekara Daya Ko Biyu Ko Uku Ba, Amma Saikaga Suna Ta Shiga Groups Kuma Suna Yawan Posting A Cikin Wadannan Groups.

To Ko Shakka Babu Idan Kana Aikata Irin Wadannan Abubuwa Wata Rana Zaka Iya Tashi Kaga Facebook Sun Dakatar Da Account Dinka, Sai Muce Allah Ya Kiyaye.

Abu Na Uku Shine, Barayin Account, Wadannan Mutane Suna Matukar Damun Yawancin Masu Amfani Da Facebook, Domin Da Zarar Sun Sakaka A Gaba To Ko Basu Kwace Wannan Account Naka Ba To Zasu Jawo Facebook Suyi Blocking Dinsa.

To Hanyar Da Zaka Kubuta Daga Hannun Ire-iren Wadannan Mutane Shine, Ka Tabbata Sunan Daka Bude Account Dinka Shine A Jikin National Id Card Dinka.

To Idan Kayi Haka Zasu Bukaci Kasa National Id Card Dinka, Daga Nan Saisu Budema.

Abu Na Karshe Shine Posting Wadanda Basu Daceba Irin Posting Din Banza Ko Yaki Ko Rigima, Faceboom Basa Son Irin Wadannan Posting Din.

A Takaice Dai Wadannan Sune Muhimman Abubuwan Da Sukesa Facebook Suyi Block Na Account Dinka Batare Da Kasan Cewar Ga Abinda Kayiba Ko Ga Abinda Yake Faruwa.

Mungode Mungode Saimun Hadu Daku A Darasi Na Gaba Inda Muke Fatan Zaku Kasance Da Wannan Shafi Namu Mai Albarka Mungode.

Advertisement

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Advertisement
Back to top button
error: Alert: Content selection is disabled!!