Tutorials

Yadda Zaka Kalli Status Din Abokinka Ko Abokiyarka A Whatsapp Batare Da Yasan Cewa Ka Kallaba.

Advertisement Join Our Whatsapp Group

Yadda Zaka Kalli Status Din Abokinka Ko Abokiyarka A Whatsapp Batare Da Yasan Cewa Ka Kallaba.

Jama,a Assalamu Alaikum Barkanmu Da Wannan Lokaci Sannunmu Da Sake Saduwa Daku A Cikin Wannan Shafi Namu Mai Albarka Hikimatv.

Inda A Darasin Namu Nayau Zamu Kawo Muku Cikakken Bayani Akan Yadda Zaka Hana Kowa Sanin Cewar Ka Kalli Status Dinsa.

Amma Kafin Mukai Gayi Muku Cikakken Bayani Zamu Bukaci Dakayi Kokari Ka Saurari Ko Ka Karanta Wannan Bayani Tundaga Farko Har Karshe Domin Fahimtar Yadda Abin Yake.

To Da Farko Dai Idan Kanaso Ka Kalli Status Na Wata Ko Wani Daga Cikin Abokanka Kuma Bakaso Yasan Cewar Ka Kalli Wannan Status Nasa.

Saika Danna Wurin Da Aka Akayi Wasu Alamu Guda Uku Can Daga Sama Hannunka Na Dama, Bayan Ka Danna Wannan Wuri Zasu Mikaka Zuwa Shafi Na Gaba Inda Daga Chan Kasa Zakaga Wani Wuri Da Aka Rubuta.

Setting, Bayan Ka Danna Wannan Wuri Daga Sama Zakaga Wurin Da Aka Rubuta Account, Kana Danna Wannan Wuri Saika Kara Danna Wurin Da Aka Rubuta Privacy.

Bayan Ka Danna Kan Privacy To Daga Kasa Zakaga Wurin Da Aka Rubuta Read Receipt To Saika Danna Wannan Wuri Kana Dannawa Wurin Zai Rufe To Yana Rufewa Shikenan Ka Gama.

Zaka Iya Bude Status Nakowace Yarinya Ko Saurayi Batare Da Yasan Cewar Ka Buda Status Dinsaba.

Mungode Mungode Mungode Inda Dukka Dukka Anan Muka Kawo Karshen Wannan Darasi Wanda Yazo Muku Kai Tsaye Daga Shafin Hikimatv.

Muna Rokon Kadda Ku Manta Da Danna Mana Alamar Allow Da Kuke Gani A Duk Lokacin Da Kuka Shiga Wannan Shafi Namu, Domin Danna Wannan Alama Shine Zaisa A Rika Turo Muku Sako Da Zarar Mun Saki Wani Sabon Darasi Mungode.

Advertisement

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Advertisement
Back to top button
error: Alert: Content selection is disabled!!