Tutorials

Yadda Zakayiwa Wani Transfer Din Data ( MB ) Zuwa Layin Wayarsa Koda Bakwa Tare.

Advertisement Join Our Whatsapp Group

Yadda Zakayiwa Wani Transfer Din Data ( MB ) Zuwa Layin Wayarsa Koda Bakwa Tare kai koma dai bai sani ba matukar kasan numbar wayarsa.

Jama,a Assalamu Alaikum Barkanmu Da Wannan Lokaci Sannunmu Da Sake Saduwa Daku A Cikin Wannan Shafi Namu Mai Albarka Hikimatv.

A Darasin Namu Nayau Zamu Kawo Muku Cikakken Bayani Akan Yadda Zakuyi Transfer Na Data Zuwa Ga Wasu Wadanda Kukeso Ko Suka Bukaci Ku Tallafa Musu Da MB.

Abinda Mukeso Shine Ku Tsaya Ku Karanta Wannan Bayanin Dalla-dalla Domin Ku Fahimci Yadda Abin Yake Domin Tsallake Wani Wuri Zai Iya Zamo Sanadiyyar Samun Matsalarku Wajen Yin Wannan Aiki.

To Da Farko Dai Abinda Yakamata Kasani Sai Da Kudi Ake Samun Kudi, Ma,ana Saika Sayi Abu Mai Kyau Zaka Samu Riba Mai Kyau.

Abinda Nake Nufi Dai A Takaice Shine Datar Daka Saya Idan Ta Welcome Back Ce Bazatayi Ba, Dalili Shine Ita Wannan Data Duk Da Saya Kayi Tamkar Bunus Take.

Saboda Haka Sai Dai Kasayi Active Data, Ita Active Data Ana Sayan Tane Ta Hanyar Danna 1311#.

Idan Ka Danna Wannan Code Zaka Iya Sayan Data Ka Kuma Turawa Wani Wanda Kakeson Turawa Amma Sai Dai Zasu Iya Baka Adadin Mb Din Dazaka Tura A Ranar Ko A Wannan Lokaci.

Saboda Haka Abinda Yakamata Kayi Shine Ka Sayi Data Mai Kyau Domin Kasamu Saukin Turawa Wani.

To Idan Kuma Kanaso Ka Sayawa Wani Ne Wannan Data To Kai Tsaye Zaka Danna Wannan Code Na 1311# To Idan Kayi Reply Da Yanayin Mb Din Da Zaka Saya Misali.

Kanaso Ka Sayi Mb Din Da Zaiyi Kwana Daya Ya Kare Ko Kwana Bakwai Ko Wata Daya, To Saika Zabi Wanda Kake Son Saya.

Bayan Kayi Reply Da 1,2, Ko 3 Wato Na Kwana Daya Ko Sati Daya Ko Wata Daya, Saika Zabi Wacce Zaka Saya Ta Dari Daya Ko Dari Biyu Ko Biyar Ko Dubu Daya Kai Koma Wacce Kake Son Saya.

To Bayan Kayi Reply Da Wannan Number Zai Kaika Shafi Na Gaba Wanda A Wannan Shafi Ne Zakaga Wurin Da Zakayi Reply Da Su Dinga Sayama Bayan Kasaya A Wannan Karo ? Ko Kuma Sau Daya Kake Son Saya Wanda Shine Na Biyu A Kasa Kuma Zakaga Wani Wuri Da Aka Rubuta.

Buy For A Friend, A Hausance Shine Kasayawa Abokinka To Anan Idan Wani Zaka Sayawa Saika Danna Ko Kayi Reply Da Wannan Number Ta Buy For A Friend, Daga Nan Saika Saka Number Din Wanda Zaka Turawa Daga Nan Saika Kara Maimaita Number Din Daga Nan Kana Taba Send Saika Jira Second Uku Zuwa Goma Zai Tafi Indai Kana Da Adadin Kudin Da Kasayi Wannan Data.

Idan Kuma Sayan Datar Kayi Kana son Katurawa Wani Wani Abu Daga Cikin Wannan Datar Taka To Kai Tsaye Saika Danna 131Phone number*Data amount# To Kana Dannawa Shikenan Datar Zata Tafi, Amma Wata Kila Ba,a Tura Kasa Da 500mb Zuwa Sama.

Mungode Mungode Mungode Saimun Hadu Daku A Wani Sabon Darasin Anan Gaba Sannan Kadda Ku Manta Da Danna Mana Alamar Subscribe Domin Samun Sabbin Darussa Mungode.

Advertisement

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Advertisement
Back to top button
error: Alert: Content selection is disabled!!