Tutorials

Yadda Zaka Maida Video Zuwa Audio Wato Mp4 To Mp3 Ta Hanyar Amfani Da Mp3 Old Video Converter.

Advertisement Join Our Whatsapp Group

Yadda Zaka Maida Video Zuwa Audio Wato Mp4 To Mp3 Ta Hanyar Amfani Da Mp3 Old Video Converter.

Jama,a Assalamu Alaikum warahamatullahi wabarakatuhu barkanmu da sake saduwa daku Acikin wannan shafi namu mai albarka hikimatv.

Acikin darasin namu nayau zamu kawo muku cikakken bayani akan yadda zaka maida video, zuwa audio, koda kuwa videon waka ne ko film koma dai videon minene to zaka maidashi audio batare da wani bata lokaci ba.

Sannan wani abun burgewa dangane da wannan application shine cikin sauki zakayi wannan aiki, misali idan videon wakar da kake so ka maida zuwa audio 50Mb ne, to idan ka maidashi audio to zai koma 5Mb Ko 8Mb Kaga Ansamu Sauki Sosai.

Dukkan wadannan abubuwa munayinsu ne domin ku idan babu ku to muma babu mu saboda hakane muke fatan zaku rika kawo ziyara izuwa cikin wannan shafi namu domin samun sababbin shirye-shiryenmu akowane lokaci.

Sannan domin mu saukaka muku yadda zaku samu wannan application zamu ajiye muku link dinsa a kasan ko a karshen wannan bayani.

Saboda haka saiku karanta bayanin a nutse kuma tun daga farko har karshe domin ku fahimci bayanin sosai, domin tsallake wani wuri yana iya zamowa sanadin ka kasa yin wannan abu yadda yakamata.

To da farko dai bayan kayi download na wannan converter mai suna Mp3 video converter, zakayi installing nata, daga nan saikayi open dinta to daga hannun dama chan daga sama zakaga wani wuri da aka rubuta ” SELECT ” to saika danna wannan wuri.

Bayan ka danna wannan wuri zai kawoka kai tsaye izuwa kan file manager na wayarka, kai zaima watsoma dukkan videon dake kan wayarka ko memory dinka.

Kai wani karin abin farin ciki da jindadi dangane da wannan application din shine kana danna wannan wuri mai suna Select zai watsoma videon da aka turama ko kayi download dinsu a wannan sati da kake ciki.

To bayan ka duba videon da kake son maidata audio saika danna kan videon daga nan zai dawo dakai baya wato zasu dawo dakai cikin farkon wannan application inda zaka duba wurin da aka rubuta ” Convert ” to kana danna wannan wuri cikin abinda baifi 5 seconds ba wannan wakar ko videon zai koma audio.

Kaga wannan wata hanyace wadda tafi kowace hanya sauki wurin maida video zuwa audio ammafa ta hanyar amfani da application.

Mungode Mungode Sai munhadu daku acikin wani sabon darasin dangane da wayoyin android,sims, computers, da sauran ilimin zamani.

Ga link din da zaku danna domin saukar da wannan application zaku danna wurin da aka rubuta ” Download Mp3 Converter Now ” Domin samun damar mallakar wannan application din cikin sauki.

Download Mp3 Old Video Connverter Now

Advertisement

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Advertisement
Back to top button
error: Alert: Content selection is disabled!!