Tutorials

Yadda Zaka Saukar ( Download ) Na Kowane Film India ( Bollywood ) Nollywood, Da American Film ( Hollywood ) Ta Hanyar Amfani Da Telegram.

Advertisement Join Our Whatsapp Group

Jama,a Assalamu Alaikum Barkanmu Da Sake Saduwa Daku A Cikin Wannan Shafi Namu Mai Suna Hikimatv.

A Cikin Darasin Namu Nayau Zamu Kawo Muku Cikakken Bayani Akan Yadda Ko Hanyar Dazakabi Domin Sauke Ko Muce Download Na Fina-finan India, Chanise Film, Nigerian Films, Tare Da American Films.

Saiku Karanta Wannan Bayani Tun Daga Farko Har Karshe Domin Fahimtar Abin Yadda Yakamata Domin Tsallake Wani Wuri Ko Bangare Zai Iya Zama Sanadin Da Zakayi Kuskure A Wurin Yin Wannan Aiki.

To Da Farko Dai Abinda Ake Bukata Shine Application Na Telegram Wanda Zamu A Jiye Muku Link Dinsa A Kasa Wato A Karshen Wannan Bayani Ko Ince Darasi Namu.

Hanya Ta Biyu Dazaka Iya Samun Wannan Application Shine Ta Hanyar Download Dinsa A Manhajar Google Playstore, Sannan Zaka Iya Rubuta Telegram A Google Ta Hanyar Amfani Da Opera Mini, Ko Chrome Ko Uc Browser, Amma Dai Inaga Hanya Mafi Sauki Shine Kuyi Download Dinsa Ta Link Din Dana Ajiye Muku Ko Kuma Ta Playstore.

Wadannan Hanyoyi Guda Biyu Wato Playstore Dakuma Link Din Dana Ajiye Muku Yafi Download Ta Google Sauki Damin Download Ta Google Yana Da Matukar Wahala Dakuma Bata Lokaci.

Sannan Bugu Da Kari Bakowane Ya Iya Download Ta Google Ba, Amma Idan Ta Playstore Ne Zaka Iya Yi Cikin Sauki Kuma Nasanma Mafi Yawancin Wasu Daga Cikinku Suna Da Manhajar Telegram Ko Ince Application Din Telegram Kaga Idan Kana Dashi Basai Ka Kara Download Din Saba.

To Bayan Ka Saukar Da Wannan Application Ko Muce Manhaja Ta Telegram Saikayi Install Dinta Akan Wayarka Bayan Kayi Installing Saikayi Open Na Application Din Bayan Kayi Open Wato Ka Shiga Cikin Wannan Application Zakaga Wurin Da Akace Kasa Phone Number Dinka.

Sannan A Wannan Wurine Zaka Zabi Kasarka Wato Code Number Da Kasarka Take Amfani Dashi Wanda Shine +234 To Bayan Kazaba Saikasa Phone Number Dinka, Wato Numbar Wayarka, Bayan Kasa Zasu Kiraka, Wato Zasu Kira Wannan Number Daka Saka Domin Su Tabbatar Dacewar Wannan Number Tana Aiki.

To Kadda Ka Daga Wannan Kira Ka Barsu Kiran Da Kansa Zai Katse, Idan Ya Katse Shikenan Zai Wuce Dakai Zuwa Cikin Wannan Application, To Anan Saika Taba Alamar Profile Kasa Hotonka Da Sunanka, Daga Nan Kagama Register.

To Daga Sama Hannunka Na Dama Zakaga
Wurin Da Zakayi Search Na Abubuwa To Saika Danna Wannan Wuri Karubuta Sunan Film Din Dakake So Take Zasu Kaika Site Ko Ince Channel Din Da Suke Dora Irin Wadannan Fina-finai.

Sannan Bugu Da kari Bawai Channel Daya Zasu Nunama Ba, A,a Zasu Nunama Channel Da Damane, To Saika Rika Shiga Kowanne Kana Dubawa Har Kasamu Wanda Suka Dora Wannan Film Da Kake Nema Kana Ganinsa Zaka Danna Wurin Wata Yar Kibiya Ko Gun Download Shikenan Kaga Kasamu Wuri Mai Sauki Wanda Zaka Rika Saukar Da Films Cikin Sauki.

Ga Link Din Wannan Application Na Telegram Amma Kai Kana Iya Searching Dinsa A Manhajar Playstore Domin Ka Dauko Latest Version Wato Sabo Wanda Bai Kusa Expire Ba.

Kai Tsaye Saika Danna Download Telegram Now Domin Saukar Da Wannan Application Zuwa Kan Wayarka.

Download Telegram Now

Advertisement

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Advertisement
Back to top button
error: Alert: Content selection is disabled!!