Tutorials

Yadda Zaka Dorawa Whasapp Dinka Email Tare Da Fingerprint Saboda Kaucewa Sabuwar Hanyar Da Barayi Ke Amfani Da Ita.

Advertisement Join Our Whatsapp Group

Jama,a Assalamu Alaikum Warahamatullahi Barakatuhu, Barkanmu Da Sake Saduwa Daku A Cikin Wannan Shafi Namu Mai Suna Hikimatv.

A Cikin Darasin Da Zamu Kawo Muku Yau Zamu Kawo Muku Cikakken Bayani Ne Akan Yadda Zaku Kare Whatsapp Dinku Ta Hanyoyi Guda Biyu.

Sai Dai Hanya Ta Farko Tafi Karfi Domin Ita Hanyace Wadda Babu Yadda Za,ayi Wani Ya Sacema Whatsapp Matukar Dai Ba Asiri Yayima Ba.

HanyaTa Biyu Kuma Hanyace Wadda Zaka Kare Account Dinka Daga Budurwarka Koma Duk Wasu Masu Daukan Wayarka.

To Bari Mu Fara Bayani Akan Hanya Ta Farko Saboda Muhimmancinta Wadda Ita Wannan Hanya Zaka Kare Whatsapp Dinka Ne Daga Kowane Irin Mutum Wanda Yakeson Rabaka Da Wannan Account Naka.

( 1 ) – Hanya Ta Farko.
Hanya Ta Farko Dai Itace Hanyar Da Zaka Kare Ko Ka Tsare Whatsapp Dinka Ta Hanya Sanya Gmail Dinka Akan Wannan Whasapp Naka Ta Yadda Babu Yadda Za,ayi Wani Ya Iya Hawa Matukar Baisa Wannan Gmail Ba.

Koda Kuwa Kaine Kasanja Waya To Idan Kazo Login Ko Hawansa Akan Wannan Sabuwar Wayar To Dole Ne Saika Dora Wannan Gmail Din Kuma Ka Sanya Password Idanma Ka Manta Password Din To Zasu Turoma Takan Gmail Din Saika Zubashi Shikenan Zaka Iya Hawa Kayanka.

To Yadda Zakayi Idan Kanason Dora Wannan Gmail Shine, Sai Dai Kuma Tayiwu Shi Whatsapp Din Da Kake Amfani Dashi Bashi Da Wannan Security Wato Tsaro A Hausance.

Idan Kuma Yana Dashi To Shikenan Idan Kuma Bashi Dashi Saika Nemi Gb Ko Adwhasapp Duk Wadannan Suna Da Wannan Security Ko Ince Tsaro To Da Farko Abinda Zakayi Shine.

Zaka Taba Wata Alamar … Guda Uku Daga Can Saman Hannunka Na Dama A Cikin Home Din Whasapp Dinka Daga Nan Zai Watsoma Shafi Na Gaba Anan Saika Danna Wurin Da Aka Rubuta Setting, Daga Nan Zai Kaika Wani Shafin Da Zaka Danna Wurin Da Aka Rubuta ” Account” To Anan Zakaga Wurin Da Aka Rubuta 2-Step Verifications.

To Anan Saika Danna Kan Wurin Da Aka Rubuta 2-step Verifications Daga Nan Zaibaka Damar Da Zaka Saka Gmail Dinka Bayan Kasa Zasu Turoma Code Saika Zuba Daga Nan Shikenan Babu Wanda Ya Isa Yahauma Kan Whatsapp Dinka.

Sai Dai Idan Kai Kabashi Wannan Gmail Naka Ko Kaika Cireshi Daga Kan Wannan Whasapp Naka.

Sai Hanya Ta Biyu Wanda Bata Wuce Kare Kanga Daga Harin Yan’mata Ko Abokanka Masu Shiga Harkar Dabata Shafesu Ba.

( 2 ) Ita Kuwa Wannan Hanya Itace, Hanyar Da Zaka Saka Fingerprint Akan Whasapp Dinka Ta Yadda Babu Wata Ko Wani Dazai Hauma Kansa Batare Da Yardar Kaba.

Ita Kuwa Wannan Hanya Idan Kanason Ka Dora Fingerprint Dinnaka Da Farko Zaka Danna Alamar … Guda Ukun Nan Kamar Yadda Kayi A Farko Bayan Ka Danna Saika Danna Kan Setting Idan Ka Danna Kan Setting Saika Danna Privacy, Bayan Ka Danna Privacy Zakaga Wurin Da Aka Rubuta Fingerprint Lock Saika Danna Wannan Wurin To Daga Nan Zaka Saka Fingerprint Dinka.

Shikenan Ka Gama Duk Sanda Ka Fita Daga Cikin Application Din Whasapp Ka Dawo To Dole Saika Saka Fingerprint, Sannan Shi Whatsapp Din Zai Rika Tambayarka Password Din Daka Saka A Lokacin Daka Sa Gmail Dinka Bayan Sati Daya Ko Sama Da Sati Daya Abinda Yakamata Shine Ka Rike Numbobin Daka Zaba Saboda Tsaro.

Mungode Mungode Mungode Inda Dukka Dukka Anan Muka Kawo Karshen Wannan Darasi Inda Muke Fatan Zaku Kasance Da Wannan Shafi Namu Mai Suna Hikimatv A Kowane Lokaci.

Advertisement

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Advertisement
Back to top button
error: Alert: Content selection is disabled!!