Yadda Zaka Ajiye Numbobin Wayar ka A Facebook
Assalamu Alaikum Warahamatullah, Barkanmu da sake kasancewa daku a wannan shafin namu mai Albarka na HikimaTv.Com
A yau nazo muku da darasi akan yadda zaku ajiye dukkan numbobin da suke kan wayarku akan facebook dinku cikin sauki.
Wannan hanyar zai baka damar copy numbobinka daga kan wayarka zuwa kan facebook naka koda kuwa sunkai 10,000 ba tare da ka rasa ko daya ba.
Da farko ka tabbatar kana da Facebook Account.
Saika bude shi kaje menu nasa
Idan ya bude sai kayi can kasa ka shiga inda aka rubuta Settings
Sannan ka sakeyin kasa ka shiga Inda aka Rubuta Upload Contacts
Daga nan zakaga Inda aka rubuta Upload contacts Sai ka kunna shi
Daga nan zai kawo maka wani shafi saika danna inda aka rubuta Turn On
Daga nan zai sake kawo maka wani shafi wanda anan zakaga yana upload na dukkan number dake kan wayarka, saika jira ya gama upload din
Da zarar ya gama zakaga ya kawo maka Add Friends sai kayi kasa ka shiga inda aka rubuta Skip
Daga nan shikkenan ka gama dora dukkan lambobin da suke kan wayar ka.
Yanzu kuma sai yadda zakaga dukkan Lambobin daka dora a facebook din naka:
Shima Zaka sake shiga facebook din sai kaje setting sai ka kara shiga “Upload contact” bayan ya bude saika duba daga kasa zakaga rubutu blue inda aka rubuta “See contact you’ve uploaded in messenger”
Bayan ya bude sai ka duba daga kasa zakaga inda aka rubuta “See contact you’ve upload from facebook”
Anan ne zakaga dukkan jerin lambobin daka dora
Domin duba number saika shiga Show Contact Information.
Allah ya bada sa’a