Yadda Zaka Tsayar da Applications din da Suke Sha Maka Data
Net Blocker wani app ne da zai baka damar tsayarda kowanne app da ke amfani da internet idan kana ra’ayin hakan.
A misali baka son a dinga ganinka online a WhatsApp, Facebook, Twitter ko Instagram
Da zarar ka zabi kowanne app kakeso ya daina a aiki a cikin wannan manhajar nan take zai tsaya har zuwa lokacin da kaga dama ka bude.
Kada rubutun yayi yawa sosai
Ba dogon rubutu danna nan domin sauke application din
👇
Download Now
Zai kaika Play store inda zaka sauke app din.
Bayan ka sauke zaka shiga cikin app din sai ka duba daga kasa zakaga On/Off sai ka mayar da shi On domin ya Fara aiki.
Zakaga jerin apps din da ke kan wayarka, sai ka zabi Wanda kakeso ya daina aiki da internet sai ka danna alamar internet sake gefen app din sai kawai ka fito.
idan kayi haka tamkar ka saka wannan app din Flight Mode ne, Koda ka shiga app din da ka kulle bazaiyi aikiba har sai ka koma cikin Net Blocker din ka Kara Danna alamar internet din domin kayi unlock nashi.
Idan zaka bama wani wanda kasan yana shanyema data Kuma bakasan hakan wayarka sai kawai kayi block apps dinka gaba daya koda ya Bude data ba inda zai bude.
Allah yasa mu dace🙏