Tutorials

Yadda Zaka Hada Wakoki Kamar Ashirin ( 20 ) Ka Maidasu Remix Ta Hanyar Amfani Da Audio Lab.

Advertisement Join Our Whatsapp Group

Jama,a Assalamu Alaikum Barkanmu Da Wannan Lokaci Sannunmu Da Sake Saduwa Daku A Cikin Wannan Tasha Tamu mai suna Hikimatv.

A cikin posting din da zamu kawo muku ayau zamu kawo muku cikakken bayani akan application din da zaku iya hada wakoki remix wato ka hada waka kamar guda goma ka kuma maidasu remix ta hanyar amfani da wannan application din mai suna audio lab.

Ku karanta wannan bayani gaba daya kuma a nutse domin sanin yadda zakuyi amfani da wannan application.

To da farko dai ana bukatat wannan application mai suna audio lab kafin ka fara wannan aiki, zaka iya samun wannan application a manhajar google, sannan zaka iya saukar dashi daga manhajar google playstore dake kan wayarka.

Amma domin mu saukaka muku zamu ajiye muku link dinsa a chan kasa ko muce a karshen wannan bayani namu domin kusamu saukin download nasa izuwa kan wayoyinku.

To da farko dai bayan ka tabbatar dacewar ka saukar da wannan application mai suna audio lab saika budeshi ka shiga cikinsa.

Shi wannan application da kuke ganinsa yana da abubuwa da dama wadanda akalla sunkai guda goma kawai dai mun dauko wadannan guda biyun ne kachal zamu kawo muku cilakken bayani akansu.

Kana shiga cikin wannan application zakaga abubuwa da dama irin su…

Trim Audio, Mix Audio, Merge Audio, Tag Editor, Record Audio, Split Audio, Da Dai Sauransu To Anan Zamu Muku Bayani Akan Guda Biyu Ne Na Farko Shine ” Merge Audio” Wato A Hausance Hada Audio Ko Muce Hada Wakoki Zaka Iya Hada Wakokin Da Kake So Koda Sunkai Guda Talatin Ko Hamsin A Wuri Daya Kafin Daga Baya Ka Maidasu Remix.

Idan ka shiga wurin da aka rubuta merge audio zakaga sun watsoma duk wakokin da suke kan wayarka, to idan ka taba guda daya zasu kaika wani shafin inda anan daga kasa zakaga alamar + Plus saika tabata anan zasu baka damar ka kara zabar wata wakar to kaga a haka a haka zaka rika zabar wakoki kana danna + Plus har sukai adadin yadda kake so daga nan zakaga wata alama a dan sama wadda tanuna arrow tana kallon sama, saika danna wannan alamar daga nan zaiyi converting ya hadema su wuri daya.

Daga nan saikayi back ka dawo baya saika zabi ” Speed Changer” Da hausa wato changer saurin waka dakuma rage mata sauri.

To anan saika zabi wannan wakokin daka hade saika danna kansu daga nan zai kaika shafi na gaba anan zakaga alamu biyu a tsakiya idan zaka karawa wakar sauri saika tabashi zuwa gaba idan kuma zaka rage mata sauri saika jashi zuwa baya daka saita saika danna alamar play dake chan gefe a hannun dama, daga nan zaiyi searching yayi converting saikayi back ka kunna wakar ka kaji yadda ta koma remix.

Danna Wurin Da Aka Rubuta Download Audio Lab Now Dake Kasa Domin Saukar Da Wannan Application.

Download Audio Lab Now

Mungode mungode mungode kadda ku manta da danna alamar allow na notifications domin samun sababbin shirye-shiryenmu a kowane lokaci.

Advertisement

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Advertisement
Back to top button
error: Alert: Content selection is disabled!!