Sanarwa ta musamman ga Wanda Suka Cike Tallafin kudi Na NG-CARES
Jama’a Assalamu Alaikuma Barkanmu da sake kasancewa daku a wannan shafin namu mai Albarka HikimaTv.
Idan baku mantaba a kwanakin baya am fitar da wani sabon shiri na Ng Cares wanda hukumar zata bayar da tallafi domin taimakawa matasa da kudi domin su dogara da kansu, Wanda mutane dayawa suka cike tun a wancan lokacin.
To a yanzu haka hukumar tana sanar da duk wanda suka cike tallafin na Ng cares kan cewa a yanzu haka sun fara turawa wasu daga cikin wanda suka nema wani sako wanda yake dauke da Link wanda zaka shiga Link din domin ka karasa cike sauran bayananka.
Wannan shine irin sakon da suke aikowa:
Idan har kaga sun turo maka wannan sakon to karka gogeshi domin yana da muhimmanci, abun da zakayi kawai shine: Ka duba cikin sakon akwai wani Link wanda zaka danna kansa anan take zai kaika shafin da zaka cike dukkan abunuwan da suke bukata.
Amma ka lura dakyau, zasuyi tambaya shin kana da CAC, zasu cema Yes ko No, saika danna No, idan kuma kana da akwai saika danna Yes.
Note: Kuyi sani cewa dole sai idan sune suka gayyaceka sannan zaka samu damar samin sakonnan idan har basu turo maka sakon ba, to karka kuskura ka shiga Link din domin kowa da nasa. Dan haka idan basi turo makaba karka damu domin kowa za,a turo masa insha Allah.
Allah ya bada Sa’a