Yadda Zaka Ajiye Images, Videos, Musics, Applications Akan Gmail Dinka Yadda Koda An Sacema Wayarka Zaka Iya Dawo Dasu.
Assalamu Alaikum Barkanmu Da Wannan Lokaci Sannunmu Da Sake Jamewa Daku A Cikin Wannan Sabon Posting Na Yadda Zaka Ajiye Dukkan Wani Abu Dayake Cikin Wayarka Ta Android Akan Gmail Dinka Ka Kuma Samu Damar Dawo Dashi Koda An Sace Wayarka Gaba Daya.
Saikuyi Kokari Ku Karanta Wannan Bayani Gaba Daya Domin Ku Fahimci Yadda Zakuyi Wannan Aiki Batare Da Kunsamu Wata Matsala Ba.
To Da Farko Dai Zaka Shiga Cikin Wayarka Bayan Ka Tabbatar Da Cewar Gmail Dinka Yana Kan Wayartaka.
To Bayan Ka Shiga Cikin Main Menu Na Wayarka Idan Baka Ganewa Mi Ake Nufi Da Main Menu Ba, To Ina Nufin Cikin Application Din Da Suke Kan Wayarka Gaba Daya Wato Home Na Wayarka.
Bayan Ka Shiga Wannan Wuri Saika Nemi Application Mai Suna ” Drive ” Amma Fa Ka Tabbata Datar Wayarka A Bude Take Kuma Kana Da Mb Adadin Yawan Abubuwan Da Zaka Ajiye, Misali Idan Zaka Ajiye Hotuna Wanda Nauyinsu Yakai 100 Mb To Dole Ne Yazamo Kana Da 100Mb Akan Layinka Na MTN Kona Airtel Kafin Ka Fara Wannan Aiki.
Idan Kuma Kasan Baka Da Wannan Mb To Koka Farama Bazaka Gamaba Mb Dinka Zai Kare Saboda Haka Saika Kula, Sannan Dole Saida Data Ake Ajiye Wadannan Abubuwa A Cikin Wannan Application Mai Suna Drive.
To Idan Ka Kabbatar Da Cewar Kana Da Mb Mai Yawa Wanda Zaka Iya Ajiye Dukkan Abubuwan Da Kake Bukata Saika Bude Datar Wayanka, Bayan Ka Bude Datan Wayarka, Saika Shiga Home Na Wayarka Wato Cikin Apps Din Wayarka, Bafa Ina Nufin Ta File Manager Ba, A,a Ta Farkon Wayarka.
Domin Idan Kahau File Manager Din Kanwayarka Ma Bazaka Samu Drive Ba, To Bayan Ka Samo Drive A Cikin Apps Din Wayarka Saika Shiga Cikinsa, Idan Ka Shiga Cikinsa Zai Iya Neman Kadan Bashi Dama, Saika Bashi Daga Nan Zakaga Wata Alama Ta + Plus A Kasa Wato Alamar Add Ka Dora Wani Abu Kenan A Hausance.
To Da Zarar Kaga Wannan Alama Saika Danna Ta Daga Nan Zata Baka Wasu Alamu Guda Shida, Wadannan Alamu Dai Suna Kamar Haka…
Folder, Upload, Scan, Google Docs, Google Sheets, Google Slides.
To Da Zarar Kaga Wadannan Folders Saika Zabi Ta Farko Wato Folder, Amma Fa Sai Idan Kanason Kayi Create Na Folder Din Da Kake Son Ajiye Wani Abu, Misali.
Idan Kana Son Ajiye Hotuna, Wato Pictures, Saika Kirkiri Folder Mai Suna “My Images”
Idan Kuma Video Zaka Ajiye To Zaka Iya Create Na Folder Mai Suna ” My Video” Haka Zalika Idan Kanason Ajiye Wakoki Ne Wato Musics A Turance Saikayi Create To Ka Kirkiri Folder Mai Suna “My Audio” Idan Kuma Applications Zaka Ajiye Saika Kirkiri Folder Mai Suna “My Applications”.
To Kaga Idan Kayi Haka Abin Zai Zamo Cikin Tsari Yadda Komi Kazo Dubawa Ko Dawo Dashi Kan Wayarka Daga Baya Koda An Sacema Wayarka To Zaka Ganeshi Cikin Sauki Batare Da Kana Ta Nemansa Cikin Daruruwan Abubuwan Daka Ajiye Ba.
Idan Kuma Bakason Bata Lokaci Wurin Create Wato Kirkiran Folders Zaka Iya Kai Tsaye Danna Wurin Da Aka Rubuta “Upload” , Kana Danna Wannan Wuri Shima Zai Iya Neman Permission Wato Kabashi Dama Kenan A Turance, Idan Kabashi Dama Zai Kaika Izuwa Cikin File Manager Din Kan Wayarka Inda Kake Ajiye Komai Da Komai Na Wayanka.
To Kaga Anan Saika Nemi Folder Ko Wurin Da Kake Ajiye Wakoki, Videos, Pictures, Ko Application Din Da Kake Son Ajiyewa.
Bayan Ka Shiga Folder Misali Ta Hotuna Saika Danne Kan Hoto Na Farko Zaiyi Alamar Mark Wato Zaka Iya Hada Hoto Dari Ko Dubu Ka Ajiyesu Zuwa Daya A Cikin Wannan Drive Ko Ince Gmail Na Wayanka.
To Bayan Kayi Selecting Da Hausa Kazabi Abubuwan Da Kake Son Boyewa Saika Danna Select, Daganan Zakaga Sun Fara Alamar Uploading Ko Ince Downloading.
Daga Nan Saika Dan Jirasu Batare Daka Rufe Datan Wayankaba, Har Su Gama Hawa Kan Gmail Din Naka, Bayan Sun Gama Zaka Iya Budesu Daya Bayan Daya Kana Ganinsu Don Gudun Kadda Kayi Aikin Banza.
Bayan Sun Gama Hawa Zaka Iya Fita Daga Cikin Wannan Application Kai Tsaye Batare Da Wata Damuwa Ba, Domin Karika Kayi Safe.
Tabbas Baka Da Wata Damuwa Game Da Hotunanka Ko Videos Dinka Ko Apps Dinka Ko Wakokinka Muddin Ka Ajiyesu A Cikin Wannan Application Mai Suna Drive, Domin Da Zarar Ka Sayi Wata Wayar Ka Dora Wannan Gmail Naka Daka Dora Akan Waccan Wayar To Kana Shiga Cikin Wannan Application Na Drive Zaka Tarar Da Komai Naka Daka Ajiye A Wancan Karon.
Kuma Wani Abun Farin Ciki Shine Zaka Iya Download Nasu Zuwa Kan Wayanka, Sannan Kuma Still Dai Suna Nan A Cikin Wannan Drive Naka Wato Kan Gmail Naka.
Mungode ! Munhode !! Mungode !!!.
Inda Dukka Dukka Anan Muka Kawo Karshen Wannan Darasi Na Yadda Zaka Ajiye Dukkan Wani Abu Da Kake Bukata Akan Wayarka Ta Android Ka Kuma Dawo Dashi Koda An Sacema Wayanka.
Saimu Hadu A Posting Na Gaba Wanda Shikuma Zamu Kawo Muku Cikakken Bayani Akan Yadda Zaku Ajiye Numbobin Wayanku Akan Gmail Koda Sunkai Guda Dubu Goma Ka Kuma Samu Damar Dawo Dasu Zuwa Daya Koda An Sacema Waya Koka Rasa Layin Wayanka.
Domin karin bayani: Shiga nan